Shugaban Amurka Joe Biden ya shaida wa takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi ta wayar tarho cewa kasarsa ba za ta amince a tursasa wa Falasdinawa fita daga yankin Gaza da aka mamaye ba, ko kuma Gabar Yammacin Kogin Jirdan, kamar yadda wata sanarwa daga Fadar White House ta bayyana.
“Shugaban kasa yana mai tabbatar da shirinsa na kafa kasar Falasdinawa da kuma jaddada muhimmancin rawar da Masar za ta taka wajen ganin an bi wadannan ka’idoji,” in ji White House.
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Biden ya bayyana jin dadinsa “game da kokarin Masar na kulla yarjejeniyar sakin mutanen da Hamas ta kama tare da tsagaita wuta a Gaza.”
2205 GMT — Isra’ila ta ‘kashe’ ɗan babban dan majalisar Hezbollah
An kashe ɗan wani babban dan majalisar dokokin Hezbollah a wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon, kamar yadda wata majiya ta kusa da danginsa ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
Majiyar wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, “Abbas Raad, ɗan shugaban majalisar dokokin kungiyar Hezbollah Mohammed Raad, “an kashe shi ne tare da wasu ‘yan kungiyar Hezbollah ” a wani harin da Isra’ila ta kai a wani gida a Beit Yahun.
Kamfanin dillancin labarai na Labanon ya rawaito cewa, “wani hari ta sama da maƙiya Isra’ila suka kaddamar kan wani gida a Beit Yahun, ya kashe mutane hudu tare da jikkata wasu daban.
Daga bisani kungiyar Hezbollah ta ce harin da Isra’ila ta kai kan wani gida a kauyen Yahun ya kashe mayakanta biyar ciki har da dan babban dan majalisar dokokin Hezbollah.
Amurka ta kama wasu jiragen yaki marasa matuka da aka harba daga Yemen: Pentagon
Amurka ta kama wasu jiragen sama marasa matuka da aka harba daga yankunan da ke karkashin ikon Houthi a Yamen, in ji rundunar tsakiya, CENTCOM.
An harbo jiragen ne a lokacin da jirgin yakin Amurka ke sintiri a Tekun Maliya. Jirgin da ma’aikatan jirgin ba su lalace ko jin rauni ba, “in ji CENTCOM a shafin X.
Source: TRTHausa