Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana takwaransa na Rasha Vladimir Putin a matsayin shugaban kama karya wanda ke fama ta takunkumin karya tattalin arziki da kuma kadaici, sakamakon yadda kasashen duniya suka kauracewa kasar sa inda yake cewa duniya na yaki ne tsakanin mulkin dimokiradiya da kuma kama karya.
Shugaban ya ce ma’aikatar shari‘ar Amurka na kafa wani kwamitin ko ta kwana na musamman wadda za ta bincike laifuffukan da shugabannin Rasha ke aikatawa domin daukar matakai a kan kasar.
Biden ya ce suna hada kai da kawayensu na kasashen Turai domin kwace kasaitattun gidaje da lambunan da attajiran Rasha suka mallaka tare da jiragen sama na kansu wadanda suke shawagi da su zuwa kasashen duniya.
Shugaban wanda ya dauki dogon lokaci a jawabin nasa na sa’a guda yana tsokaci akan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ya ce suna daukar matakai da dama a kan kasar inda ya ce, “kuma a daren yau ina shaidawa jama’ar kasar mu cewar na bi sahun kawayenmu na duniya wajen rufe sararin samaniyar Amurka ga daukacin jiragen saman Rasha”.
‘Yan majalisun Amurka sun yi ta tashi suna yi wa Biden tafi lokacin da yake gabatar da jawabin a zauren majalisar dokoki.
A wani labarin na daban Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta amince da wani tsarin da zai iya kaiwa ga matakin karin farashin man fetur duk kuwa da hauhawar farashin danyen man da kuma kalubalen da ke taka rawa a kasuwannin duniya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce kasashen da Saudiya da Rasha ke jagoranta za su kara yawan man da suke hakowa da ganga 400,000 a kowace rana a cikin watan Maris, tare da kiyaye manufofin da aka yi a watannin baya.
Masana tattalin arziki sunce tuni kungiyar ta OPEC mai mabobin kasashe 23 ke fafutukar ganin ta cimma kason da ta ke da shi da wasu kasashe kamar Angola da Najeriya da ba za su iya habaka hanyoyin hako da man ba da sauransu kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba.
A cikin watan Disamba, jimillar adadin albarkatun da OPEC ke fitarwa ya karu da ganga 90,000 a kowace rana, wanda haura 400,000 da ake son cimmawa, a cewar wani bincike na kamfanin dillancin labarai na Bloomberg.
Masana dai na ganin kasuwar ta kara samun habaka ne sakamakon tashe-tashen hankulan da suka addabi jiga-jigan kasashen da ke samar da mai, wato Rasha, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A ranar Litinin ne Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake kakkabo wani makami mai linzami da ‘yan tawayen Huthi na Yaman suka harba, wanda shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai wa kasar, wadda ke cikin kawancen sojan da Saudiyya ke jagoranta.
A Turai, zaman dar-dar tsakanin Rasha da kawayenta na Yamma ya kai matsayin mafi girma tun bayan yakin cacar-baka bayan da fadar Kremlin ta tara sojoji a kan iyakarta da Ukraine.