Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umurnin mika wasu takardu dake kunshe da bayanan da suka shafi tarzomar magoya bayan magabacinsa Donald Trump a majalisar dokokin kasar a ranar 6 ga watan Janairu ga kwanitin Majalisar dake gudanar da bincike akai.
An kafa wannan “kwamiti na musamman” na Majalisar Wakilai don tantance rawar da Donald Trump ya taka a harin da magoya bayansa suka kai ginin majalisar dokokin kasar na Capitol, yayin da ake tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.
Tsohon shugaban ya yi amfani da damar karfin ikon shugaban kasa wajen hana mika takaddun da suka danganci rikicin magoya bayansa a Capitol don kauce mika su ga kwamitin binciken.
To sai dai a ganin Joe Biden ta bakin kakakin Fadar White House Jen Psaki bai halasta ayi amfani da ikon shugaban kasa ba wajen hana mika bayanan ga kwamitin bincike.
Shugaban na ganin yana da matukar mahimmanci ga Majalisa da Amurkawa su gane komai dangane da abubuwan da suka faru a ranar 6 ga watan Janairun wannan shekara ta 2021, domin hana sake faruwar haka nan gaba.
A wani labarin na daban shugaban kasar Amurka Joe Biden yace tsohon shugaba Donald Trump ba zai dinga samun bayanan asiri daga hukumomin tsaro ba, kamar yadda aka saba baiwa tsaffin shugabanin kasa saboda halayen sa na rashin tabbas.
Shugaban yace bayanan asirin ba zasu kara ma Trump komai ba, sai dai bashi damar tsegunta su ga jama’a.
Wannan zai zama karo na farko da za’a daina baiwa tsohon shugaban kasa irin wadannan bayanai na asiri domin sanin halin da kasar ke ciki.
Kasar Amurka na da al’adar gabatar da bayanan tsaro na sirri ga tsoffin shugabannin domin sanin halin da ake ciki a koda yaushe.
A shekaru 4 da yayi a karagar mulki, Donald Trump yayi ta takun saka da hukumomin tsaron kasar, abinda ya sa ya sauya shugabannin hukumar leken asirin kasa har sau 6.
Trump ya kuma ki amincewa da rahotan hukumar leken asirin kan cewar kasar Rasha tayi katsalandan a zaben shekarar 2016 wanda ya bashi damar samun nasara.