Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran sa na Amurka Joe Biden sun amince su gudanar da wani taro a tsakanin su muddin Rasha bata mamaye Ukraine ba domin rage tankiyar da ake samu da kuma kaucewa barkewar yaki.
Wani babban jami’in gwamnatin Faransa yace bangarorin biyu ne zasu bayyana lokacin da za’ayi taron da kuma wurin gudanar da shi, yayin da ake saran ya kunshi masu ruwa da tsakaki akan rikicin Ukraine.
Wannan gagarumin ci gaba ya zo ne bayan da Amurka ta bayyana cewar, Rasha ta kammala duk wani shirin da ya kamata domin mamaye Ukraine, yayin da kasashen biyu suka zargi juna saboda musayar rokoki.
Rahotanni sun ce akalla mutane 500 suka shiga zanga zanga a Birnin Madrid dake Spain domin nuna rashin amincewar su da yunkurin mamaye Ukraine.
Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya yi ikirarin cewa zai zama abin kunya idan har kungiyarsa ta gaza kammala gasar firimiyar bana a sahun ‘yan ukun saman teburi dai dai lokacin da mai horarwa Ralf Rangnick ke kokarin dawo da tawagar turbar nasara biyo bayan rashin abin kirki a wasanni da dama da ya kai ga sauya manaja.
Babu dai wata gagarumar nasara tun bayan maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer da Rangnick ya yi inda yanzu haka kungiyar ke matsayin ta 7 a teburin Firimiya tazarar maki 22 tsakaninta da Manchester City jagora.
Sai dai Ronaldo na Portugal mai shekarau 34 wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta Ballon d’Or har sau 5 ya ce dolensu ne matsayin ‘yan wasan kungiyar su sauya tunani tare da jajircewa don ganin basu yi abin kunya a karshen kaka ba.
Kalaman na Ronaldo na zuwa bayan shan kayen da United ta yi a hannun Wolves da ya janyowa kungiyar caccaka inda dan wasan ke cewa a zuciyarsa ya na ganin tabbas za su iya kammala firimiya matsayin na 2 ko na 3 ko da basu iya dage kofin a wannan karon ba.
Acewar Ronaldo bai zo firimiya don karkare kaka a matsayin na 6 ko na bakwai ba fatansa shi ne sake dage kofin firimiya tare da tsohuwar kungiyar tasa kuma har zuwa yanzu bai karaya ba.
A wani labarin na daban Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya yi ikirarin cewa zai zama abin kunya idan har kungiyarsa ta gaza kammala gasar firimiyar bana a sahun ‘yan ukun saman teburi dai dai lokacin da mai horarwa Ralf Rangnick ke kokarin dawo da tawagar turbar nasara biyo bayan rashin abin kirki a wasanni da dama da ya kai ga sauya manaja.