Jamus za ta ci gaba da barin tashar sufurin jiragen samanta na soji a Yamai a bude a mataki na wucin gadi, kamar yadda ma’aikatar tsaro a Berlin ta bayyana a yammacin jiya Talata, jim kadan bayan da Tarayyar Turai ta sanar da kawo karshen aikin soji a kasar nan da ranar 30 ga watan Yuni.
Berlin na da sojoji kusan 90 da ke Yamai a halin yanzu. Har zuwa juyin mulki a shekarar 2023, Nijar ta kasance kawa ga kasashen yammacin duniya da ke yaki da mayakan da suka kashe dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.
Sai dai kuma mahukuntan sojan kasar sun matsawa Faransa tsohuwar mulkin mallaka da ta janye dakarunta tare da amincewa da janye sojojin Amurka, inda ta kuma kara kulla alaka da Rasha.
Ma’aikatar tsaron Jamus a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce “Jamus da Nijar sun kulla yarjejeniyar wucin gadi da za ta ba da damar ci gaba da kasancewar sojojin Jamus a Nijar,” in ji ma’aikatar tsaron Jamus, inda ta kara da cewa hakan zai bai wa Berlin damar bude sansanin tun daga ranar 31 ga watan Mayu a yanzu.
Tun a shekara ta 2013 ne dai Jamus ta yi amfani da sansanin da ke Yamai a matsayin cibiyar samar da kayan aiki ga dakarunta a makwabciyarta Mali inda suke aiki a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, MINUSMA.
A wani labarin na daban rundunar Ƴansandan ta ƙasa reshen jihar Gombe ƙarƙashin jagoranci CP Hayatu Usman psc ta samu nasarar kama masu satar ƙarfen hanyar jirgin ƙasa wato (Railway Track Sleepers)
Hukumar ta samu nasarar damke mutane huɗu ne da ake zargi da cirewa tare da satar ƙarfen tarogon jirgin ƙasa a ranar 29/05/2024 da misalin ƙarfe 8:40pm, bayan samun bayanan sirri daga mutanen gari.
Waɗanda ake zargin sun haɗar da:
Ibrahim Yauta mai shekaru 30 da ke Unguwar Uban Doma Liji Yelmantu da Kasimu Umar mai shekaru 26 mazaunin Bogo garin – Waziri bye-pass, sai kuma Yusuf Mohammed mai shekaru 32 da ke Kofar Sarkin Liji, da kuma Shu’aibu Saidu Unguwa Uku, Gombe.
DUBA NAN: ‘Yan Achaba Sun Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Legas
Matasan an kama su ne ɗauke da ƙarafunan hanyar jirgin ƙasa guda 42 a cikin motar ɗibar yashi/bulo a inda bayan tuhumarsu suka amsa laifinsu tare da bayyana sunan waɗanda suke sayarwa idan sun sato mai suna Shu’aibu Saidu mazaunin Unguwa Uku, Gombe.