Tauraron Real Madrid Karim Benzema ya barar da damar bugun fanareti har sau biyu, yayin karawarsu da kungiyar Osasuna jiya Laraba gasar LaLiga.
David Alaba, da Marco Asensio da kuma Lucas Vazquez ne suka ci wa Madrid kwallayenta uku, yayin da Darko Barasanac ya ciwa Osasuna guda.
A halin yanzu Madrid na da maki 78 inda ta baiwa mai biye da ita ta biyu Atletico Madrid mai mai 61 tazarar maki 17 a teburin LaLiga, bayan da Atleticon ta tashi canjaras 0-0 babu ci tsakaninta da Granada.
Kwallayen da Karim Benzema ya ci wa Real Madrid ya basu damar doke Chelsea da kwallaye 3-1, nasarar da ta sanya masu rike da kofin gasar zakarun Turai shiga tsaka mai wuyar ficewa daga gasar zakarun Turai a matakin Kwata Final.
A bangaren Chelsea, Kai Havertz ne ya rage tazarar da aka samu da kwallo 1 tilo da ya ci wa kungiyar ta sa.
Wani abu da ya dauki hankali yayin wasan dais hi ne yadda golan Chelsea Edouard Mendy ya yi kuskuren da ya baiwa Benzema damar jefa kwallo ta uku a ragarsu.
Wannan ne karo na biyu da Benzema ya ci kwallaye uku cikin wasa guda wato Hat-trick a turance, cikin gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da shi kadai ya ci kwallayen uku a karawarsu da Paris Saint-Germain a wasa na biyu na zagayen da ya kunshi kungiyoyi a gasar Zakarun Turai.
Sai a ranar 12 ga watan Afrilun nan Chelsea za ta yi tattaki zuwa birnin Madrid domin sake karawa da abokiyar hamayyar ta a karo na biyu.
Kofin gasar zakarun Turai na karshe da Real Madrid ta lashe shi ne na 13 a shekarar 2018.