Kwallayen da Karim Benzema ya ci wa Real Madrid ya basu damar doke Chelsea da kwallaye 3-1, nasarar da ta sanya masu rike da kofin gasar zakarun Turai shiga tsaka mai wuyar ficewa daga gasar zakarun Turai a matakin Kwata Final.
A bangaren Chelsea, Kai Havertz ne ya rage tazarar da aka samu da kwallo 1 tilo da ya ci wa kungiyar ta sa.
Wani abu da ya dauki hankali yayin wasan dais hi ne yadda golan Chelsea Edouard Mendy ya yi kuskuren da ya baiwa Benzema damar jefa kwallo ta uku a ragar su.
Wannan ne karo na biyu da Benzema ya ci kwallaye uku cikin wasa guda wato Hat-trick a turance, cikin gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da shi kadai ya ci kwallayen uku a karawarsu da Paris Saint-Germain a wasa na biyu na zagayen da ya kunshi kungiyoyi a gasar Zakarun Turai.
Sai a ranar 12 ga watan Afrilun nan Chelsea za ta yi tattaki zuwa birnin Madrid domin sake karawa da abokiyar hamayyar ta a karo na biyu.
Kofin gasar zakarun Turai na karshe da Real Madrid ta lashe shi ne na 13 a shekarar 2018.
A wani labari na daban Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya jinjina wa dan wasan gaban kungiyar, Karim Benzema, bayan da dan kasar Faransan ya zura kwallaye biyu a raga a wasan La Liga tsakaninsu da Cadiz, lamarin da ya kai su ga darewa saman teburin gasar.
Zidane ya bayyana farin ciki da bajintar da Benzema ke nunawa, yana mai bayyana shi a matsayin dan wasa mai mahimmanci a kungiyar, wanda ba kawai yana cin kwallaye ne ba, yana kuma taimaka wa dimbim ‘yan wasa su na haskawa.
Benzema ya ci kwallon farko a wasan ne ta wajen bugun daga – kai – sai – mai – tsaron – raga, karon farko da Madrid ke samun irin wannan bugun tun a watan Oktoban 2020.
Ya kuma taimaka Alvaro Odriozola ya ci kwallonsa ta farko a babbar gasar La Liga.
Nasarar ta kai Real saman teburin La Liga da maki 70 a gaba da Atletico Madrid, wadanda suka buga wasanni kasa da Real din.