Benin Na Tattaunawa Da Rwanda Domin Yaki Da Ta’addanci.
Kasar Benin, ta fara tattaunawa da Rwanda ta yadda zata taimaka mata da kayan aiki akan yaki da ta’addanci mai nasaba da mayakan dake ikirari da sunan jihadi a arewacin kasar.
Kakakin gwamnatin Benin, ya ce, kasar na karfafa ayyukan sojinta, domin karya laggon gungun kungiyoyin dake kai masu hare hare daga kasashen makobta Nijar da Burkina.
Wilfried Houngbédji Ya ce, kamar da Nijar da Burkina, suna tattauna da Rwanda domin samun tallafi na yaki da mayakan dake kaiwa sojoji hari.
Tun da farko dai an rawaito daga wata kafa ta Africa Intelligence, cewa ana tattaunawar sirri tsakanin Kigali da Cotonu, game da batun jibge daruruwan sojoji da kwararu na Rwanda a arewacin Benin.
Saidai daga bisani ma’aikatar tsaron Rwanda ta ce ba zatayi bayanni ba kan batun, amma tan amai tabbatar da cewa akwai alaka ta fuskar tsaro tsakaninta da Benin.
READ MORE : Ingila; Ranar Litini Za’ayi Jana’izar Elizabeth II.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen bakin teku, irinsu Benin, Togo, Ghana da Ivory Coast, ke cewa suna karfafa matakan sojojinsu a iyakin Mali, Nijar da Burkina Faso game da barazarar dake akwai ta mayakan dake ikirari da sunan jihadi.