Sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya gabatar bayan yanke hukuncin daurin shekaru 25 da aka yi wa Paul Rusesabagina ta bayyana matukar damuwa dangane da yadda aka gudanar da shari’ar, inda take cewa rahotanni rashin adalcin da ke fitowa daga Rwanda abin dubawa ne.
Ita ma kasar Belgium ta bayyana irin wannan matsayi akan Rusesabagina wanda ta bayyana shi a matsayin dan kasarta, inda ta yi watsi da hukuncin.
Ministar harkokin wajen Belgium, Sophie Wimes ta ce duk da bukatar da kasar ta yi ta gabatar wa hukumomin Rwanda, sun yi watsi da su wajen yanke masa hukunci ba tare da yin adalci ba.
Ita ma ‘yar tauraron fina-finan, Carine Kanimba ta ce dama sun san yadda hukuncin zai kaya, kuma alakalan kotun sun bayyana abinda shugaban kama karyar kasar ke bukata.
A wani labarin na daban shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi afuwar wasu ‘yan Algeria a madadin kasar sa, wadanda aka yi watsi da su, bayan da suka taimakawa Faransa wajen yakar masu neman ‘yancin kan kasar ta su da ke arewacin Afirka.
Fiye da ‘yan Algeria dubu 200 ne suka taimakawa sojojin mulkin mallaka na Faransa a yakin da suka gwabza da mayaka masu neman ‘yanci kasar ta Algeria daga shekarar 1954 zuwa 1962.
Bayan Karkare yakin da bangarorin biyu suka fafata da ya kunshi cin zarafi gami da azabtar da dubban mutane ne, gwamnatin Faransa a waccan lokacin ta yi watsi da mayakan sa kan da suka yi mata biyayya da aka fi sani da Harkis duk da alkawuran da tayi a baya cewa za ta kula da su, matakin da ya jefa su cikin kunci.
Kididdiga ta nuna cewar bayan karewar yakin neman ‘yan cin kan Algerian a ranar 18 ga watan Maris na 1962, mayakan Harkis dubu 42 ne kawai hukumomin Paris suka baiwa damar komawa Faransa wasunsu tare da iyalansu, yayin da kuma aka bar kimanin mayakan sa kan dubu 90 a Algeria, matakin da ya baiwa sabbin shugabannin kasar damar yiwa akasarinsu kisan kiyashi, a matsayin daukar fansar cin amanar kasar su da suka yi.
A shekarar 2001, masu fafutukar kare hakkin dan adam da suka yi yunkurin ganin an hukunta gwamnatin Algeria kan laifukan yakin da ta aikata, sun yi ikirarin cewa mayakan na Harkis dubu 150, shugabannin waccan lokaci suka kashe a kasar ta Algeria, a matsayin fansar taimakawa Faransa.
Bincike dai ya nuna a halin yanzu, iyalan mayakan sa kan da suka taimakawa Faransa yayin yakin neman ‘yancin Algeria akalla dubu 400 ke zaune a sassan kasar da ta yiwa kakkaninsu mulkin mallaka.