An fara gudanar da cikakken zama na biyu na kwamitin koli karo na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da yammacin yau Lahadi 26 ga wata a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda babban sakataren kwamitin kolin, Xi Jinping, ya gabatar da rahoton aiki a madadin ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis.
Zaman dai zai gudanar da bincike kan daftarin shirin yin garambawul ga hukumomin jam’iyyar kwaminis da na kasa baki daya, da takardar jerin sunayen mutanen da ofishin siyasar ya bada shawarar su zama shugabannin kasa ga taro na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, gami da sunayen mutanen da ya bada shawarar su zama shugabannin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, ga taro na farko na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin. (Murtala Zhang)
A wani labarin na daban stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, takardar matsayar kasar Sin game da warware rikicin Ukraine a siyasance, wata muhimmiyar gudummawa ce. Yana mai cewa, kiran da aka yi na kaucewa amfani da makaman nukiliya yana da matukar muhimmanci.
A jiya Juma’a ne, kasar Sin ta fitar da wata sanarwa, inda a cikinta ta bayyana matsayinta kan batun sasanta rikicin kasar ta Ukraine a siyasance, tana mai cewa tattaunawa ita ce kadai mafita mafi dacewa wajen warware rikicin na Ukraine.(Ibrahim)
Source:LeadershipHausa