An bude yanki na farko na hedkwatar kungiyoyin kimiyya da fasaha na kasa da kasa a birnin Beijing, a jiya Laraba.
Zuwa yanzu, yankin wanda kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasar Sin da gwamnatin birnin Beijing suka gina, ya ja hankalin kungiyoyi 8, ciki har da kungiyar Society for Digital Earth, mai rajin amfani da sabbin fasahohin domin amfanin duniya da kuma kungiyar International Hydrogen Fuel Cell Association masu samar da makamashin Hydrogen.
A cewar Shu Wei, jami’in kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasar Sin, manufar yankin ita ce hada nasarorin da Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha da nasarorin da sauran sassan duniya suka samu a fannin, cikin aminci.
Shu Wei ya kuma bayyana yakinin wannan yanki zai saukakawa masana kimiyya da fasaha na kasar Sin shiga ana damawa da su a harkokin duniya. Haka kuma zai bayar da gudunmuwa wajen tsare gaskiya da tabbatar da aminci da hadin gwiwa a tsakanin masana kimiyya da fasaha na kasashen duniya. (Fa’iza)
A wani labarin na daban a ranar Litinin 29 ga watan Mayu 2023 aka rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Jagaban kasar Borgu a matsayin shugaban tarayyar Nijeriya na 16, a bikin da aka yi a dandalin ‘Eagle Skuare’ da ke Abuja.
Tabbas Tinubu ya zama shugaban kasa ne a daida lokacin da Nijeriya ke kan siradi mai fuskoki da dama.
A kan haka ne masana a bangarorin rayuwa dana tattalin arzikin kasa da dama suka yi hasashen irin namijin aikin da ke a gaban sabon shugaban kasa.
Shigowar Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya ya kawo karshen mulkin shekara 8 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, kamar yadda ‘yan Nijeriya suka yi ta zumudi a farkon mulkinsa, haka ma a halin yanzu ‘yan Nijeriya a ciki wajen kasa na zumudin ganin kamun ludayin Sabon shugaban kasa, Tinubu wanda ya yi alkawarin zai magance tulin matsalolin da ke fuskantar kasar nan, a sabon takensa na sabunta fata ga ‘yan Nijeriya (Renewed Hope).
Cikin jan aikin da masanan da masu ruwa da tsaki suka tsamo a matsayin abubuwan da ya kamata Tinubu ya fara fuskanta da zaran ya daidaita a kan kujerar shugabancin kasa sun hada da, matsalar tsaro, tattalin arziki, wutar lantarki, gine-gine, kiwon lafiya, ilimi, da aikin gona.
Matsalar tsaro
Na farko daga cikin jan aikin da ke fuskantar Jagaban, Tinubu shi ne matsalar tsaro, wadanda suka hada da ayyukan ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, ta’addanci, satar man fetur, ‘yan tawaye, fadace fadacen kungiyoyin matsafa, rikicin manoma da makiyaya, kashe kashe da fadace fadace a tsakanin al’umma, ayyukan masu damfara ta intanet, daga cikin manya manyan abubuwan da ake fuskanta a bangaren matsalolin tsaro a kasar nan.
Kowane bangare 6 na kasar na da nashi irin matsalar tsaron da yake fuskanta, wannan yana kuma faruwa ne duk da kokarin da sojoji suka tafka na ganin sun kawo karshen ayyukan ‘yan ta’addan gaba daya a cikin shekarun da suka gabata.
Misali, yankin arewa maso yammancin Nijeriya da arewa ta tsakiya na fuskantar matsalolin ‘yan ta’adda da masu garkwua da mutane. Matsalar sace-sacen man fetur kuma ya ta’azzara ne a yankin Neja Deltada yankin kudu maso kudancin Nijeriya.
Bincike ya nuna cewa har yanzu ana fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso gabas sakamakon ayyukan ‘yan Boko Haram.
Masu ruwa da tsaki a bangaren harkar tsaro da wakilimu ya tattauana da su sun bayyana cewa, lallai za a iya yin maganin wadanna matsalolin amma sai in sabuwar gwamnatin nan ta daura damarar yin haka, ta hanyar amfani da dukkan karfinta.
Wani kwarrare a bangaren tsaro mai suna Abdullahi Umar ya lura da cewa, yana da muhimmanci sabuwar Gwamnatin Bola Tinubu ta samar da kwamiti na musamman na kwarraru da za su fitar da hanyar magance wannan matsalar tun daga tushenta.
Ya kuma bayar da shawarar a sauya fasalin tsarin samar da tsaron da ake tafiya da su a halin yanzu, ya ce, baragurbi a cikin jami’an tsaro na kawo cikas ga yadda ake yaki da mastalar tsaro, ya kuma kamata a tabbatar hukunta duk wanda aka kama da hannu a yi wa lamarin zagon kasa.
Wani masanin harkar tsaron kuma mai suna, Sunday Oni, ya bayyana cewa, ya kamata Sabon Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi aiki tare da majalisar kasa wajen fitar da dokokin da za su tabbatar da duk wani mai shanu ya samarwa kansa wajen kiwo tare da killace shanayensa don kada su shiga hakkin sauran al’umma.
Ya kuma yi kira na musamman ga ‘yan majalisa da su samjar da dokar da zai ba sarakunanmu na gargajiya hurumi a kundin dokokin kasa ta yadda za su yi aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankunan su, ta haka za a iya kawo karshen rikice-rikice a tsakanin al’umma.
Tallafin Man Fetur Da Batun Wutar Lantarki
Batun cire tallafin man fetur da kayyade farashin albarkatun man fetur da kuma bukatar samar da man fetur din a wadace ga al’umma na daya daga cikin matsala na gaggawa da gwamnatin Tinubu za ta fuskanta da zaran ya daidata a kan karagar mulki bayan da ya sha rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu 2023.
A bangaren abin da ya shafi samar da wutar lantarki, dole Sabon Shugaban kasa Tinubu ya nemo hanyar da zai kara yawan wutar lantarkin da ake samu a Nijeriya daga megawatts 4,500 zuwa yadda al’umma za su amfana da shi yadda ya kamata ba kamar yadda yake a halin yanzu ba inda wutar baya isan kowa da kowa duk kuwa da kudaden da suke karba a hannun mutane.
Tsohon shugaban kasa Muhamadsu Buhari ana gab da kammala wa’adinsa na mulki ya kafa wata karkarfar kwamiti da ta hada da wasu mambobin sabuwar gwamnatin nan don su tattauawa tare da nemo mafita ga lamarin janye tallafin man fetur daga nan zuwa karshen watan Yuni, ana wata daya da darewar Tinubu karagar mulki.
Zuwa yansu gwmanati ta tabbatar da kashe fiye da Naira Tiriliyan 6 a cikin kasa da watanni 18 amma ‘yan Nijeriya na ci gaba da fuskantar karancin Man duk kuwa da karin farashin Man da aka yi daga naira 165 a kan lita daya zuwa Naira 195 a kan lita daya a cikin kasa da shekara daya.
Masana sun bayyana cewa, ana bukatar Tinubu ya dauki tsatsaurar mataki a kan abin da ya shafi tallafin man fetur ta yadda za a bar masu harkar man fetur su rika fita suna sayo man a kasashen waje ba wai lallai sai su saya a hannun Kamanfanin Mai na NNPC ba.
A halin yanzu da aka kaddamar da matatar mai na Dangote ana sa ran za a samu saukin matsalolin da ake fuskanta, don yanzu kamfanin NNPC na iya sayen man a hannun kamfanin Dangote da ke Legas maimakon yadda take dogara da sayo man daga kasashe kamar su Amsterdam da Belgium daga kamfanonin mai irin su Shell da Mobil.
Basukan Naira Tiriliyan 77
Da zaran sabon Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya leka bangaren tattalin arzikin kasa a yayin da ya fara gudanar da mulkin kasar nan, abin da zai fara gani shi ne tulin bashin da ake bin Nijeriya wanda suka kai Naira Tiriliyan 77 wannan kuma sun hada ne da wadanda ake bin gwamnatin tarayya da jihohin kasar nan gaba daya, kudin ruwan basukun sun kai kashi 22 daga cikin dari.
Wani abin mamaki a nan kuwa shi ne a daidai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ke shirin barin karagar gwamnati ya kuma ciwo bashin tiriliyan 77 a kan gwamnati mai kamawa sai gashi yana sake mika bukatar a bashi izini ya cin bashin Dala 800 daidai da Naira Miliyan 330 daga Bankin Duniya, wannan kuma yana zuwa ne bayan ya samu izinin karbar bashin dala miliyan 800 a matsayin kudin tallafi da za a ba ‘yan Nijeriya sakamakon cire tallafin Mai da za a yi a nan gaba.
Wadannan tulin basukan da aka tara a kan Nijeriya, masana sun ankarar da cewa, a na gaba kadan kashi 90 na kudaden da ke shigowa wa kasar za a rinka amfani da sune wajen biyan basukan da albashi, abin da zai iya hana aiwatar da duk wani aiki na ci gaban al’umma.
A kwanakin baya, gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da ma’aikatan jihar cewa a yadda al’amurra ke tafiya a kasar nan in har ba a yi a hankali ba gwamnati ba za ta iya biyan albashi ba daga watan Yuni na wannan shekarar, in har ba a kai ga buga kudade ba a cikin kasa.
Gwamnatin Buhari ta ci bashin da ya kai na Naira Tiriliyan 23 a cikin gida ta hanyar Babban Bankin Nijeriya CBN, idan kuma aka hada da basukan da aka ciwo daga kasashe waje sune za su hadu su karya darajar naira ba tare da an sani ba in har ba a dauki matakin da suka dace ba.
Bangaren da al’umma suka fi jin jiki a wanna lokacin sakamakon basukan da gwamnatin Buhari ta ciwo shi ne hauhawar farashin kayyakin abinci, a haka kuma Bankin Duniya ya yi hasashen cewa, za a ci gaba da samun hauhawar farashin kayyakin abinci a wasu kasashen duniya a nan gaba.
Aikin Gona
A wannan bangaren, masana sun bayyana cewa, dole sabon shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya mayar da hankulansa a kan wasu abubuwa 6 da suka jagoranci kawo wa harkar noma cikas a Nijeriya, sun hana a samu daman cin cikakken amfanin harkar gona a Nijeriya abubuwan sun kuma hada da samar da takin zamani, Rikicin makiyayya da Manoma, rashin samun basuka daga cibiyoyin kudade, rashin samun kayyan aikin noman rani da kuma rashin samnu kayan aikin noma na zamani.
Namoma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar gona sun amince da cewa wadannan abbuwa shida sun taimaka wajen hana Nijeriya ta ci cikakken gajiyar albarkatun noma da Allah ya ajiye a kasar nan.
Shugaban kungiyar manoman Nijeriya, (AFAN) Architect Kabiru Ibrahim, ya bayyana cewa, ya kamata a karfafa yin noma a dukkan shekara ba wai sai da damuna ba, ya kuma kamata gwamnati ta zuba jari a bangaren noman rani da kuma amfani da sakamakon binciken kimiyya da fasaha da cibiyoyin bincike suka yi don samun amfani yadda yakamata ba tare da yi asara ba, kamar yadda ake yi a wasu lokutta, wannan ya zama dole in har sabuwar gwamnatin Tinubu tana son samun nasarar a bagaren noma.
“Dole sabuwar gwamnati ta gudanar da bincike don gano abubuwan da suke fi saukin nomawa a kowanne yanki na kasar nan don samar da yadda za a bunkasa yankunan tare da sanin irn tallafin da za a ba kowanne yankin ta yadda za a samu albarkatun gona yadda ya kamata, hakan kuma zai sa a san irin tallafin da ya kamata a ba kowanne yanki daidai da bukatunsa, in har aka yi amfani da wannan shawarar to a shekarar farko na sabuwar gwamnati za a ga canji mai amfai wanda zai taimaka samar da abinci ga al’umma har ma a kaiga fitarwa kasashen waje.
Kiwon Lafiya
Bangaren kiwon lafiyar kasar nan na fuskantar matsaloli da dama wanda kuma babbar kalubale ne ga sabuwar gwamnati, dole ta yi aiki tukuru in har tana son bunkasa bangaren lafiya a kasar nan, musamman inhar ana son a saukaka hanyoyin samar da kiwon lafiya a cikin sauki ga al’ummar kasa, kamar yadda Sabon shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawari ga al’umma Nijeriya a yayin da yake yakin neman zabe.
Masana sun ce, dole sabon shugaba kasa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya gaggauta dakatar da yadda likitoci ‘yan Nijeriya ke fita zuwa kasashen waje saboda rashin kulawa da albashi mai kyau a Nijeriya.
Wasu matsalolin da bangaren lafiyar kasar nan ke fuskanta sun kuma hada da karancin ma’aikata a bangaren kiwon lafiya, karancin kudade a kasafin kudin dukkan matakan gwamnati, dogaro ga tallafin da ke zuwa daga kasashen waje, yadda ‘yan Nieriya ke fita kasashen waje don neman magani, rashin aiwatar da rigakafin maganin cututtukar yara kanana a sassan kasar nan, dole sabon shugaban kasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya kawo dauki a wannan bangaren in har ana son a bangaren kiwon lafiya na kasa ya san ana yi da shi.
Ilimi
Bangaren ilimi na daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ‘yan Nijeriya suka zura ido don ganin irin matakin da Sabon shugaban kasa zai dauka a bangaren, musamman saboda yadda bangaren ya tabarbare a yan shekarun nan, matsalolin da suka addabi bangaren sun hada da yawaitar yaje yajen aiki na malaman manyan makarantun kasa, rashin isasssun kudaden aiki da kuma yawan yara da ke garanramba a tituna Nijeriya ba tare da suna zuwa makaranta ba, haka kuma karancin malama na daga cikin matsalolin da ke fuskantar bangaren ilimi da ake bukatar sabon shugaban kasa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya gaggauta kawo wa dauki da zaran ya daidaita a kan karagar mulki.
Duk da cewa, masana sun bayyana cewa, gwamnati ta gaggauta daukar matakan da suka kamata ta hanyar hada hannu da kungiyoyin masu bayar da tallafi na ciki da kasashe waje don magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren ilimi amma sun kuma ce, akwai aiki tukuru a gaban sabon shugaban kasa saboda girman matsalolin da ake fuskanta.
Masanan sun ce, sabuwar gwamnatin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu akwai bukatar kara kaimi don ganin an cike gurbin da aka samu ta yadda za a kai matakin da ake samu a makarantun kasashen duniya.
Masu ruwa da tsaki sun ce, tabbatar da an zabi wanda ya dace a matsayin ministan ilimi abu ne da yakamata sabon shugaban kasa ya yi don samun nasarar farfado da bangaren ilimin. Sun bayyana cewa, yakamata a tabbatar da an zabi masani kuma malamin jami’a wanda ya san matsalolin da bangaren ilimi ke fuskanta da yadda za a magancesu.
Dakta Ibrahim Usman Jibril da Farfesa Nasiru Medugu Idris na Jami’ar Jihar Nasarawa sun bayyana cewa, muna nukatar a dauki matakin da zai sauya fasali da halin da harkar ilimi ke ciki a halin yanzu, ta yadda al’amurra za su daidaita a bangaren ilimin Nijeriya, wannan kuma nauyi ne da ya hau kan sabon shugaban kasa.
Shi kuwa, Michael Sule, wani masani a bangaren ilimi ya ce ya kamata a tabbata an zabi malamin jami’a a mastayin ministan Ilimi kamar yadda ake yi a kasar Ghana da sauran kasashen Afrika.
Yajin Aikin ASUU
Rikicin kungiyar malaman Jami’a ta ASUU a kan gazawar gwamnatin tarayya na cika alkawarin da ta yi musu a tsawon shekaru na cikin manyan matsalolin da sabon shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai fuskanta kuma yakamata ya tabbatar da daukar matakin kawo karshensa a cikin gaggawa, domin yaje yajen aikin malaman jami’a ya dagula harkokin karatun matasanmu a ‘yan shekarun nan.
Manyan Ayyukan Da Gwamnatin Buhari Ba Ta Kammala Ba
Daya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Buhari bata kammala ba sun hada da aikin shifida hanyar jirgi na Dala Biliyan 1. 96 da ta taso daga Kano-Katsina-Jibiya zuwa Maradi wanda aka kaddamar da aikinsa a ranar 9 ga watan Fabrairu 2021.
Da shirin gina hanya jirgi mai tsawon kilo kita 284 daga Kano zuwa Maradi wanda ana sa ran zai karfafa harkokin kasuwanci a tsakanin kasar Nijar da Nijeriya, kasar Amurka da Bankin Duniya ne suke daukar nauyin aikin.
Aikin Hanyar Jirgi daga Fatakwal Zuwa Maiduguri ta Naira Biliyan 3.02
Wani aikin da yake neman kulawar sabuwar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne na aikin shifida hanyar jirgi daga Fatakwal zuwa Maiduguri na Dala Biliyan 3.02.
Saboda muhimmancin aikin ya kamata sabuwar gwmanatio ta tabbatar da daukar aikin da matukar muhimmanci.
Hanyar Jirgi Daga Kaduna Zuwa Kano
Wani aiki da ake tsammanin zai zama mai muhimmanci ga gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne na hanyar jirgi daga Kaduna zuwa kano, an dai kaddamar da aikin ne a watan Yuli na shekarar 2021, bincike ya nuna cewa har zuwa yanzu ba a kai ga kammala aiki ba kuma gashi aikin nada matukar muhimmanci ga tattalin arzikin yankin arewa gaba daya.
Wadanan na daga cikin jan aikin da ke gaban sabon shugabahn kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, masu lura da al’amurran yau da kullun suna da ra’ayin cewa in har sabuwar gwamnati ta dauki matakin da suka kamata tare da bin shawarwarin masana tabbas, gwamnatin za ta bayar da mamaki.
…Cire Tallafin Mai: Ko Tinubu Ya Fara Da Kafar Dama?
Daga Bello Hamza, Abuja
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cire tallafin Man Fetur a kasar nan har abada.
Shugaban kasa ya bayyana haka ne a dandalin Eagle Skuare, Abuja, a cikin jawabinsa bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban Nijeriya na 16 kuma shugaban rundunonin tsaron Nijeriya.
Ya yaba wa shawarar gwamnatin tshohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yadda ta tsara cire tallafin Man daki-daki, musamman ganin manyan masu kudi suka fi amfana da tallafin maimakon talakawa da aka yi abin domin su.
Tinubu ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da fitar da makudan kudade ba da sunan tallafin Mai, musamman ganin a halin yanzu hanyoyin samun kudaden shiga na gwamnati ya karanta, maimakon haka za mu karkatar da kudaden tallafin zuwa yi wa al’umma aiki a bangaren ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya.
Sai dai kuma ganin irin yadda layukan mai suka bayyana a gidajen mai kasa da sa’o’i 24 da ayyana batun cire tallafin man, wasu ‘yan Nijeriya sun fara nuna kaduwarsu game da kamun ludayin gwamnatin ta Tinubu.
Musamman masu ababen hawa da ke bin layukan mai, suna ta tayar da jijiyoyin wuya da kumfar baki tare da dora laifin abin a kan sabon shugaban kasan. Duk da cewa, masana tattalin arziki da dama sun sha nuna alfanun cire tallafin man domin bunkasa wasu sassa na ci gaban jama’a, amma kuma wasu na ganin fara gwamnatin da matsalar main a dasa alamomin tambaya cewa, ko gwamnatin ta Tinubu ta fara da kafar dama?
Wakazalika, a jawabin nasa, Tinubu ya ce, zai fito da tsarin da zai tsaftace bangaren tattalin arzikin kasa, a kan haka ya umarci Babban Bankin Nijeriya ya samar tsarin kudin canji na bai daya maimakon yadda lamarin yake a halin yanzu.
Shugaban kasa Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da amincewa, da sabbi da tsofaffin takardun naira, ya lura da cewa, duk da cewa, makasudin fito da tsarin yana da kyau amma yadda aka aiwatar da shi bai taimakawa ‘yan Nijeriya ba musamman ganin akwai ‘yan Nijeriya da dama da basu shiga tsarin banki ba.
A kan tattalin arziki, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen bunkasa kudaden shigan gwamnati tare da bayar da karfi wajen samar da aikin yi ga dimbin matasanmu, ya kuma yi alkawarin samar da tallafin kassafin kudi don dakile hauhawar farashin kayayyaki a fadin tayarra kasar nan.
Ya kuma yi alkawarin samar da wutar lantarki ga al’ummar kasar nan a cikin sauki ta yadda za a samu bunkasar kanana da matsaikaitan masa’anantu.
Ya ce, zai duba koken da masu zuba jari ke yi na yawaitar haraji da ake dora musu wanda hakan na kawo cikas ga kokarin da ake yi na jawo masu zuba jari daga kasashen duniya zuwa Nijeriya.
Ya yi alkawarin muhimmanta da lamarin a gwamnatinsa, don sai an tabbatar da tsaro a tsakanin al’umma za a iya tabbatar da bunkasar tattalhn arzikin kasa baki daya.
Tinubu, ya ce, a bangaren hulda da kasashen waje, gwamnatinsa za ta bayar da muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya a yankin Afrika ta yamma da yankin Afrika gaba daya ya yi alkawarin aiki da dukkan kungiyoyin kasa da kasa kamar su ECOWAS da AU.
Masana da masu ruwa da tsaki a bangarori da dama suka tofa albarkacin bakinsu a kan jawabin da sabon shugaban kasa Tinubu ya yi a ranar Litini 29 ga watan Mayu 2023. Sun yaba da irin kudurin sabon shugaban kasa sun kuma yi kira da a tabbatar da an aiwatar da tsare tsaren da aka shirya.
Bunkasa Da Rayuwar Siyasar Bola Ahmed Tinubu
..Yadda Ya Rika Yin Galaba A Kan Abokan Hamayyarsa
Daga Bello Hamza, Abuja
Sabon Shugaban Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai taba rashin nasara ba a takarar da ya yi na mukamin siyasa a tarihin rayuwarsa, a takarara kujerar majalisar dattawa, gwamna na kuma shugaban kasa, a kuma dukan takarar da ya yi, ya kara ne da ‘yan siyasa masu karfin gaske, wasu ma iyayen gidansa ne a siyasance, a yanayin da ya hangi alamun rashin nasara kamar shekarun 2007, 2011 da 2015, sai kawai ya goya wa wasu mutane daban baya.
Amma sai kuma ga shi aranar 29 ga watan Mayu 2023 aka ranstar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya na 16, mutumin da ya taso daga matsayin shugaban siyasar jihar Legas yau gashi ya zama shugaban Njeriya kuma shugaban rundunonin tsaron Nijeriya.
A ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 ‘yan Nijeriya suka kafa tarihi ta hanyar zabar Tinubu a mastayin shugaban Nijeriya, wannan ra’ayi ne na gaba daya al’ummar Nijeriya inda suka kadawa jam’iyyar APC kuri’unsu ta haka ne Tinubu ya yi nasara a kan sauran ‘yan takarar jami’iyyun.
Nasarar da Tinubu dan shekara 70 a duniya ya samu a zaben da aka gudanar wanda aka tabbatar da tsaftarsa, wani abu ne da kowa ya yi maraba da shi. Tinubu ya samu kuri’a miliyan 8.79 inda abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ke biye da shi da kuri’a Miliyan 6.98 yayin da Petrer Obi na jam’iyyar LP ya tashi da kuri’a miliyan 6.1.
Tinubu ya fara zuhuri a siyasar Nijeriya ne a shekarar 1992 a lokacin da ya yi takarar kujerar majalisar dattawwa mai waklitar Legas ta Yamma a karkashin jam’iyyar SDP inda ya kayar da abokiyar hamayyarsa mai suna Chif Kemi Nelson ta jam’iyyar NRC.
Daga baya ta zama na hannun daman Tiubu inda har ta zama kwamishina a lokacin da Tinubu ke gwamnan Legas a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003.
Kafin ya yi takarar majalisar dattawa, Tinubu ya so takarar majalisar wakilaa ne a mazabar ‘Lagos Island’, amma shugaban bangaren jam’iyyarsa a lokacin, Chif Dapo Sarumi ya jawo shi zuwa yankin Agege inda ya yi takarar kujerar majalisar dattawa ta Legas ta Yamma.
Kafin Tinubu ya shiga siyasa ya yi aiki a mastayin ma’aji a kamfanin mai na ‘Mobil Oil Nigeria’ inda ya kai har mastayin baban darakta.
Sunan Tinubu ya kara bayyana ne sakamakon rawar daya taka a fatutukar tabbatar da zaben 12 ga watan Yuni 1993 wanda gwamnatin Janar Babangida ta soke wanda kuma ake kyautata zaton marigayi Chif Moshood Kashimawo Olanbiwoninu Abiola na jam’iyyar SDP ne ya lashe.
Tinubu ya taka rawa a yakin da aka yi da mulkin sojoji karkashin Janar Sani Abacha wanda ya yi wa gwamnatin rikon kwarya na Chif Ernest Shonekan juyin mulki bayan da Janar Babangiga ya sauka daga mulki a ranar 27 ga watan Agusta 1993.
Bayan da Janar Abdulsalami ya dawo da tsarin dimokradiyya a shekarar 1999, Tinubu ya dawo gida inda ya shiga jam’iyyar AD, jam’iyyar da magoya bayan Awolowo suka kafa wanda kuma da ita aka yi fafutukar ‘June 12’
Tinubu da sauran ‘yan takarar gwamana a jam’iyyar AD sun samu gaggarumin nasara a yankin kudu maso yammancin kasar nan saboda sun nuna wa masu kada kuri’a cewa, suna a kan akidar siyasar marigayi Awolowo ne, a lokacin yana gamnan jihar Legas Tinubu ya kirkiro kungiyar gwamnonin yankin kudancin kasar nan inda suka fara neman hadin kan takwarorinsu na arewacin Nijeriya.
Ya kara samun farin jini ne saboda yadda yake taimakawa al’umma ba tare da la’akari da bangaranci ba.
Bayan ya bar kujerar gwmana, a shekarar 2007, Tinubu ya shiga aikin taimako da sasantawa a siyasance a fadin Nijeriya, yana kai dauki a inda ya ga ana neman zaluntar wani da ake ganin bashi da gata.
Ya fuskanci kalubale da dama a yayin da ya yi yunkurin zama shugaban kasa musamman daga wadanda ya taka rawar ganin sun zama abin da suka zama a yau, kamar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, Dabe Umahi da Rotimi Amaechi.
Duk da wadannan kalubale Tinubu ya samu nasarar da ba a yi zata ba, inda ya samu cika buruinsa na zama shugaban kasar Nijeriya.
Ba jimawa da kammala zabukan kujerun gwamnoni cikin wannan Kasa, duba da irin dalar basukan gida da na daji da sabbin zaba6bun gwamnoni za su gada daga gwamnonin da za su mika musu mulki a karshen Watan Mayun wannan Shekara ta 2023, sai aka rika yin kacibis da alkaluma gami da muryoyin masana tattalin arzikin Kasa da sauran masharhanta daga mabanbantan sakuna da lungunan wannan Kasa, na ta baje kolin hasashensu da tsinkayensu game da wadancan gadaddun basuka, daga gwamnoni masu barin gado, zuwa ga gwamnoni masu jiran gado.
Hakika masana da masharhanta sun barje guminsu na kalubalantar jerin gwanon basukan gida da na ketare da ake kan yin tozali da su, daga akalla jihohi 17 da sabbin zaba6bun gwamnoni ne za su karbi ragamar tafikad da su bayan rantsuwa. Suma sauran jihohin Kasar, ba kanwar lasa ba ne wajen hadidiyar basukan. Sai dai akasin wadancan jihohi 17, sauran jihohin, za a danganta tuhumar ciwo basukansu ne bisa wuyayen gwamnonin nasu, tun da suma sun taka mugunyar rawa ainun wajen ciwo basukan a lokacinsu. Shi kuwa sabon gwamna ko a ce sabbin gwamnoni, sun taka sawun barayi ne, don ba su hau kan kujerar mulkin jihar ba, ballantana a kwakwalo irin nasu laifukan game da yin lallaftun wadancan miyagun basuka bisa wuyayen al’umarsu.
Sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ake wa lakabi da Abba Gida Gida, na daga ‘yan sawun gaba cikin wadancan sabbin gwamnoni, wadanda suka fara numfasawa cikin kuncin takurarren numfashi game da tsirin basukan da gwamnonin da za su gada suka dankarawa jama’ar jihar tasu. Bashin gida kawai, Abba Gida Gida zai gaji bashin zunzurutun kudade ne har kimanin naira miliyan dubu dari da ashirin da biyar da ‘yan kai (N 125, 186, 662, 228. 72).
Ba ya ga wancan taragon bashi na gida, AKY Kano, zai sake gadar bashi na ketare, wanda ya tunkuyi zunzurutun mazajen kudade har kimanin dalar Amurka na gugar dala, har dala biliyan dari da tara da ‘yan kai ($ 109, 422, 176. 85). Mai yi wa, ganin wannan shuri ko a ce tsibiri na basuka, ga dukkan alamu, sune suka hana sabon gwamna Gida Gida runtsawa, awanni kalilan bayan ya lashe zaben kujerar gwamnan Kano, a karkashin jam’iyyar NNPP. An jiyo mai girma sabon gwamna na jan-hankali ne za a ce, ko jan-kunnen duk wasu mutane da ke kankajeren son kara laftawa al’umar jihar Kano sabon bashi, ta hannun gwamna mai barin gado Ganduje;
“…I will not honour any loan given to Ganduje after 18th March, 2023”.
Abba Gida Gida
A cikin harshen Hausa, wancan turanci da sabon gwamnan na Kano ya furzar cikin kaduwa da bacin rai, na nufin, “Zan yi hannun riga da duk wani bashi da za a bai wa gwamna Ganduje, bayan 18 ga Watan Mac, na Shekarar 2023)”. A takaice a nan, zaba6ben gwamna Abba Kabir Yusuf na nufin cewa, bayan 18 ga wancan Wata da aka ambata, duk wanda ya yi kirinkin bai wa gwamna mai barin gado Ganduje wani bashi, to fa sabuwar gwamnatinsu ta NNPP ba za ta bata lokaci ba wajen tunanin biyan wadannan basuka ba !!!.
A ranar da ya rage mintoci a rantsar da sabon gwamnan na Kano AKY, an ji shi yana fadin cewa, cikin kundin mulkin jihar da suka karba daga gwamnati mai barin gado ta Ganduje, sun iske wani irin tulin bashi da ake bin jihar ta Kano, wanda har suka kere tsabar kudi sama da naira miliyan dubu dari biyu da arba’in (N 240bn). Babu shakka wannan ruguntsumin taragon basuka, sun kidima Abban, ya kasa zaune balle tsaye, a karshe dai ya lashi takobin bincikar wadannan madudan basuka da aka gadarwa da gwamnatinsa;
i- Ta yaya ne ma aka ranto wadancan basuka?
ii- Mene ne gaskiyar abin da aka aikata da kudaden?
iii- Shin, babu wani wuru-wuru ko kuskunda cikin mu’amalar wadancan kudade na malala gashin tinkiya da aka ranto?
Lokaci ne kadai zai iya ba da amsar abin da zai faru tsakanin gwamnatin Abba da ta Ganduje game da batun tsirin basukan da akasarin jama’a ke kallo da wata annobar da ta yi silar karya tattalin arzikin Nijeriya karkashin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu da ta faro daga Shekarar 1999 zuwa yau (2023).
Ba sabon gwamna Abba ne kadai ya bara ba, game da tukunyar bashin da ke zabalbala a jiharsa ta Kano, sabon gwamnan Zamfara, Dauda Dare, ma da ya sami nasarar hambarar da gwamnatin Bello Matawalle, ya biyo sawu, inda yake kukan cewa, ya zo ya iske asusun jihar ta Zamfara an yi masa mugun ta’annati, an yi masa karkaf, babu kudi babu alamunsu ciki. Uwa uba kuma, an ciwowa jihar ta Zamfara wani irin mamakon tulin bashi iya wuya.
Basukan Na Kassara Kasashen Duniya Ne
Yayinda wasu Kasashen Duniya irin su Amurka ke morar basukan da suke ciwowa mutanensu, sai lamarin ya zamto akasinsa ne ke faruwa a akasarin kasashenmu na Afurka, cikinsu kuwa har da Nijeriya. A Kasashe irinsu Amurka, a kan sa irin wadancan basuka ne cikin wasu sha’anonin da za su bunkasa ne, har su sami sukunin biyan irin wadannan basuka. Misali, sanya kudaden cikin sabgar hannun jari, ko cikin wasu aikace aikacen da za su matso makudan kudade, misali, cikin sabgar lafiya, ko ilimi, ko noma da sauransu. Ta tabbata cewa, a harkar noman lemon zaki “Orange” kawai a Shekara a Amurka, a na samun kudaden shigar da suka kere adadin kudin shigar da Nijeriya ke samu a harkar man fetur a Shekara.
Babban abinda ke bai wa kowace Kasa a Duniya fursar biyan kudaden da ta ranto, bai wuce a sanya wadannan basuka cikin wasu wuraren da za su haihu, a sami ribar da za ta taimaka zuwa ga biyan bashin. A fili yake cewa, a duk sa’adda aka wayigari wata Kasa a Duniya ta yi hani’an da irin basukan da ‘yan koren jari hujja ke badawa, irinsu Bankin Ba Da Lamuni na Duniya (IMF), koko Bankin Duniya (World Bank), kuma Kasar ta gaza biya ko ta durkushe, ko tana neman durkushewa, abin da ke biyo baya shi ne, wasu tsauraran ka’idoji ne da wasu sharudda, wadanda za su kara burkuma wannan Kasa cikin bala’i da masifar kangi na tattalin arziki. Akwai misalai birjik cikin Duniya, inda za a sami jerin Kasashen da suka gwammace ma ba su karbi irin wadancan basuka ba. Idan haka batun yake, su Abba na Kano da Dauda na Zamfara, kukansu da kuma kalubalensu ga tsoffin gwamnonin jihohinsu game da mas’alar bashin na bisa tafarki ne.
Yadda IMF Da World Bank Suka Kassara Zambia
A cikin 1980s, lokacin da Kasar Zambia ke cikin haiyacinta, rayuwa na gudana be gwanin ban sha’awa, ga tallafin gwamnati a muhimman bangarorin rayuwar jama’ar Kasa, ilmin firamare da sabgar lafiya duka kyauta ne a Kasar, karkashin mulkin shugaba Kenneth Kaunda. Ga daruruwan kamfanonin gwamnati birjik a Kasa. Ga masakun saka kayaiyaki na gida gwanin ban sha’awa, a na ta kan buga harkokin samun kudade cikin rufin asiri da walwala. Kwatsam, sai farashin man fetur ya yi gwauron tashi a Duniya, sai kuma farashin ma’adinin tagulla ko a ce jan-karfe “Copper–(kofa)” ya karye warwas! Kofa, na daga manyan ma’adinai da ke samarwa da Kasar ta Zambia mamakon kudaden shiga, saboda durkushewar farashin, sai aka wayigari labari ya sha banban!
Cikin kankanin lokaci, sai abubuwa suka canja canjawa a Kasar ta Zambia, babu makawa sai bukatar yin rancen kudi daga ketare ta kama su. Da ma masana na yin nuni da cewa, daga lokacin da Kasa ta wayigari kudaden shigarta suka yi kasa ainun, hakan na tilasa ta ne zuwa ga rantar kudi. Cikin wata hira da manema labarai, shugaba Kaunda ke cewa, yanayi da yanzu ya kama mu, na, dole sai mun ranto kudi daga waje, sai dai, na tuntubi Bankin ba da lamuni da kuma Bankin na Duniya game da shin, ko za mu iya samun bashin kudi daga gare su? Sun amsa min, da me zai hana?. Bugu da kari, sun yi min alwashin cewa, babu shakka farashin kofa zai sake dagawa ba da jimawa ba. Sai dai ta tabbata cewa farashin na kofar maimakon yai kasa, sai ma kara sama ne yake yi, ba kamar yadda suka lasa masa zuma a baki ba (Analysis, June, Bol. 1 No 1, 2002 : 36).
Da lamura suka ci gaba da kwabewa a Kasar ta Zambia, bayan ciwo wadancan basuka, a karshe dai jama’ar Kasar ne suka kayar da gwamnatin Kaunda a zabe, cikin Shekarar 1991, tare da mayegurbinta da dan gwagwarmaya Frederick Chiluba, ba don komai ba, sai don a sami saukin kuncin rayuwa. Amma Ina! Sai ma wani irin curin bashin ketare ne ke neman zame musu dan-zani. Ya faru zuwa cikin Shekarar 2000, an wayigari ne a na bin Kasar Zambia zunzurutun kudade har kimanin dalar Amurka biliyan shida da digo shida ($ 6.6bn).
Dole sai da Zambia ta rika bi tana janye tallafinta daga muhimman bangarorin rayuwar jama’ar Kasa. An janye tallafin ilimin firamare kyauta, kuma an janye ma batun lafiya kyauta, saboda irin kaburin da bashin ya yi cikin Kasar kan a farga!. A dai cikin Shekarar ta 2000, gwamnatin Chiluba, ta cefanar da sama da kamfanoni mallakar gwamnatin Kasar sama da guda dari uku (300). Sannan, a hankali a hankali, hatta wuraren ma’adinan Kasar ma gwamnati ta sayar. Kuma aka wayigari, abinda gwamnati ke kashewa a harkar karatun firamare, sai ka ninka shi sau uku ne zai kai ga adadin kudaden da gwamnati ke bayarwa wajen biyan bashi a Shekara.
Shirin Ta Da Komada Na SAP “Structural Adjustment Program” A Nijeriya
Ba Zambia kadai ba, duk Kasar da tulin bashin ketare yai mata katutu ta ci gaba da hadiya shan kai, ba tare da a na sanya bashin cikin aiyukan da za su haihu ya biya kansa ba, abu na gaba da zai biyo baya shi ne, al’umar Kasa su fara dandanar kudarsu, da sunan hanya daya tilo da za a bi, don ganin an sauke wancan nauyin bashi da ya jima da danne makogwaron Kasar. Sau da yawa za a iske cewa, Turawan Yamma ne ke zuwa da irin wancan zaurance na tursasa jama’ar Kasa cikin wani sabon yanayi na kangin rayuwar.
Lokacin da kaburin basukan ketare da shugaba Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya ciwowa wannan Kasa tamu ta Nijeriya, sai hakan ya tilasa shi zuwa ga dabbaka irin wadancan matakai na janye tallafin gwamnati daga al’umar Kasa.
Lokacin da gwamnatin IBB ta zo da manufar ta da komadar tattalin arzikin Kasa na SAP, sai ya kasance saboda irin tsinkayen azabtuwa da jama’ar Kasa za su yi a sanadiyyar tsarin, sai aka rika samun jajirtattu ‘yan gwagwarmaya daga mabanbantan sako da lungu na Kasar, suna masu raddi gami da kausasa adawa ga tsarin na SAP. Duk kuwa da irin wannan soke soke da ake yi wa manufar ta SAP, hakan bai sanyaya gwiwar gwamnatin IBB ba, na ta janye manufar, maimakon haka ma, sai gwamnati ta rika bi kwararo kwararo tana kamewa tare da garkame mutanen da ke yin raddi ga manufar a gidajen yari na wasu Watanni.
A karkashin manufar SAP, akwai batun janye tallafin gwamnati daga muhimman abubuwa irinsu man fetur, harkar gona, harkar lafiya, tare da sayar da kamfanoni mallakar gwamnati ga ‘yan kasuwa, da sauran tsarabe tsarabe!