BBC, CNN da kafofin labaran Yamma sun dakatar da aiki a Rasha.
Gidajen talabijin na CNN da ABC da CBS da ke Amurka sun ce sun dakatar da yaɗa shirye-shirye daga Rasha yayin da aka ƙaddamar da wata doka da za ta hukunta masu yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda kamfanin labarai na Rasha TASS ya ruwaito.
Tun farko BBC ta ce ta dakatar da aiki a cikin Rasha amma za ta ci gaba da aiki daga wajen ƙasar.
“CBS ta dakatar da watsa labarai daga Rasha yayin da muke ci gaba da duba abubuwan da ke faruwa ga tawagarmu da take can saboda sabuwar dokar da aka kafa a yau,” a cewar CBS.
Shi ma ABC ya ce “sakamakon sabuwar dokar tantancewa a Rasha a yau, wasu daga kafofin yaɗa labarai na Yamma ciki har da ABC sun daina yaɗa labarai daga ƙasar”.
Tun farko CNN ta sanar da dakatar da yaɗa labarai daga Rasha, sai kuma kafar labarai ta Bloomberg ta ce ma’aikatanta sun dakatar da aiki a ƙasar.