Kamar yadda majiyar mu ta jiyo mana sabon shugaban kasar ta Iran ya tabbatar ta cewa bazan zauna da shugaban kasar amurka ba.
Yayin amsa tambaya daga dan jaridar Aljazeera dangane da wadansu tuhume tuhume marasa tushe da wasu daga cikin shugabannin duniya suke masa kan lamarin hakkin dan adam, sabon shugaban kasar jamhuriyar musulunci ta Iran Sayyid Ibraheeem Ra’esi ya bayyana cewa babban abin alfahari a yadda ya gudanar da rayuwar aiki wacce take cike da kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da kare hakkokin wadanda aka zalunta.
Sabon shugaban kasar ta jamhuriyar musulunci ta Iran ya tabbatar da cewa wadanda suke bayanan kare hakkin dan adam sune manyan masu take hakkin dan adam kuma ya tabbatar da cewa bazai daga ma masu zaluntar mutane ba a duk fadin duniya, dole ne jamhuriyyar musulunci ta Iran ta cigaba da ayyukan ceton al’umma wadanda aka zalunta a fadin duniya.
Sabon shugaban ya tabbatar da cewa a matsayin sa na masanin shari’a kuma tsohon alkali babban abin da ya sanya a gaba shine kare hakkin dan adam.
Dangane da ko zai iya zama da shugaban kasar amurka idan aka cirewa kasar sa takunkumin tattalin arziki yace a’a, ma’ana bazan zauna dashi ba.
Tambaya ta gaba da Sabon shugaban ya amsa daga dan jarida daga CNN itace dangane da alakar sa da shugaban kasar amurka, amsa da sabon shugaban ya bayan itace,bazan saurara ba domin abinda ya zama dole shine shugaba biden ya cika alkawuran daya dauka a kwamitin JCPOA domin al’ummar Iran basu ji dadin abinda ya faru a JCPOA din ba saboda haka babu bukatar tattaunawa a kan maganar makamashin nukiliya a yanzu har sai amurka da sauran kasashe sun aiwatar da alkawuran da suka dauka sannan Iran ma zata aiwatar da nata.
A zaman taron manema labaran dake gudana wanda ‘yan jaridar cikin gida Iran dama na kasashen waje suka halarta mai tambaya na gaba ya fito daga gidan jaridar Press T.v inda yayi tambaya a kan yadda sabon shugaban yake shirin tunkarar kokarin rayar da tattaunawar ta JCPOA inda Sayyid Ra’esi ya tabbatar da cewa kamar yadda siyasar Iran take a fili dole sai sauran kasashen da suke cikin tattaunawar JCPOA sunyi aiki da alkawuran su kafin itama Iran zatayi aiki da nata alkawuran.