Bayyana rahoton sirri kan alakar Hadaddiyar Daular Larabawa da Burtaniya dangane da kungiyar ‘yan uwa Musulmi, Hizbullah da Qatar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-jazeera, ya fitar da wani rahoto da ke bayani kan yadda hadaddiyar daular larabawa da Birtaniyya suka yi wa kungiyar ‘yan uwa musulmi, Hizbullah, Qatar da kuma Yemen bayani. Rahoton ya ambato Hadaddiyar Daular Larabawa kan taimakon dala biliyan 4 ga Burtaniya.
Takardar da Hadaddiyar Daular Larabawa da aka fallasa ta nuna cewa jam’iyyar Conservative ta Burtaniya tana da alaka a asirce da shugabannin kungiyar ‘yan uwa musulmi a birnin London kuma tana goyon bayansu, ta hanyar yin amfani da shugabannin ‘yan uwa a matsayin wani abin dogaro ga wasu kasashen yankin Gulf.
Har ila yau, tana aiki tare da Hadaddiyar Daular Larabawa, domin karfafa takunkumin da aka kakaba wa bangarorin siyasa da na Hizbullah.
Takardar da aka bankado, wanda a hakikanin gaskiya rahoton Abdullah bin Zayed ne ga Mohammed bin Zayed, ya nuna cewa ingancin kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Birtaniya da Isra’ila ya ta’allaka ne kan batun Yemen.