Bayan Shekaru Fiye Da 10 Shugaba Asad Ya Ziyarci Wata Kasar Larabawa.
Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya ziyarce kasar UAE ko hadaddiyar daular Larabawa a jiya jumma’a ziyara irinda ta fako wanda yayi zuwa wata kasar Larabawa tun fiye da shekaru 10 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jaridar Gwamnatin UAE, WAM tana fadar haka a jiya jumma’a ta kuma kara da cewa, shugaban ya gana da Yarima mai jiran gadon sarautar UAE Sheikh Mohammed bin Zayed al-Nahya, wanda ya bayyana cewa kasar Siriya itace kinshikin kasashen larabawa kuma kasar UAE a sherye take ta yi aiki tare da kasar Siriya.
READ MORE : Boris Johnson Ya Roki Saudiya Ta Ceto Duniya Daga Karancin Man Fetur.
A nasgi Bangaren shugaba Bashar Al-Asad ya bukaci kasashen larabawa su rike mutuncin kasashensu da kuma mutanennsu sannan suyi iya kokarinsu don kare yankin gabas ta tsakiya daga makiyanta.
Shugaban ya je birnin Abudhabi ne bayan da ministan harkokin wajen kasar UAE ya kai ziyara zuwa kasar Siriya yan watanni da suka gabata.