Tashar TRT Arabic ta bayar da rahoton, a wani mataki na bazata, bayan kwashe tsawon shekaru 27 an janye dokar hana saka hijabi ga mata a cikin makarantu a kasar uzbekistan.
Wannan na zuwa ne cikin wata sanarwa da minista ilimi na kasar Shirzad Shirmanuv ya fitar ne a yau, inda ya ce an janye dokar bayan ta dauki tsawon shekaru ana aiki da ita.
Ya ce matakin na zuwa ne a kokarin gwamnati na kara bayar da dama ga mutane su yi addininsu a cikin ‘yanci ba tare da takurawa ko shiga hakkinsu ba.
Sai dai da dama daga cikin masana da kuma masu bin diddigin lamurra suna ganin cewa matakin ya zo ne sakamakon sauyin da aka samu a kasar afghanistan, bayan da Taliban ta kwace iko da kasar.
Inda suke ganin cewa, gwamnatin Uzbekistan ta dauki matakin ne domin rage tayar da jijiyoyin wuya kan lamurran a suka shafi addini, domin kada ta jawo ma kanta matsala, musamman ganin cewa Taliban na makwabtaka da ita.
Tun lokacin mulkin tarayyar Soviet ne dai ake daukar matakan takura ma mutane a kasar uzbekistan kan lamurra da suka shafi addini.
A wani labarin na daban kakakin kungiyar ne Zabihullah Mujahid ya sanar da mambobin sabuwar gwamnatin da ministoci daban-daban, makonni uku bayan kwace mulki daga hannun gwamnatin Kabul.
Mullah Muhammad Hassan Akhund, daya daga cikin wandanda suka kafa kungiyar, an nada shi a mukamin Firaminista na Afghanistan.
An nada Mullah Abdul Ghani Baradar a matsayin Mataimakin fira minista.
Sauren mambobin sabuwar gwamnatin da aka sanar da nadin nasu, sun hada da Sarrajuddin Haqqani wanda zai zama ministan harkokin cikin gida, sai Mullah Yaqoob zai zama ministan tsaro, yayin da Abas Stanikzai kuma zai zama mukadashin ministan harkokin waje.
A nata bangaren gwamnatin Iran ta bayyana cewa, abin da kasar Afghanistan ke bukata a halin yanzu shi ne kwanciyar hankali da zaman lafiya.
A cikin wani bayani da ya saka a shafinsa na twitter a yau Alhamis, shugaban majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya bayyana cewa, abin da kasar Afghanistan ke bukata a halin yanzu shi ne kwanciyar hankali da zaman lafiya, tare da rashin tsoma baki na kasashen ketare a cikin harkokin kasar.
Ya ce al’ummar Afghanistan sun sha wahalhalu sakamakon shigar shugula da kasashen duniya suka yi a cikin harkokin kasarsu, wanda hakan ne babban abin da ya jefa kasar cikin mawuyacin hali tsawon shekarun da tayi kasashen yammaci na mamaye da ita.
Ya ce, Iran tana goyon bayan fifita hanyoyi na samun sulhu da fahimtar juna tsakanin al’ummar kasar Afghanistan, wanda hakan ba zai samu ba sai ta hanyar samun fahimtar juna tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar.
Daga karshe ya jaddada kira kan wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar tare da yin aiki tare domin ci gaban kasarsu, ba tare da mayar da wani bangare saniyar ware ba.