Labarai daga babban birnin jamhuriyar musulunci ta Iran na tabbatar dacewa shugaban kasar siriya shugaba bashar assad yana ziyarar aiki a kasar Iran.
A jerin wasu sakonni da shafin jagoran al’ummar Iran ya wallafa ya nuna shugaba bashar assad din a falon jagoran tare da shugaban kasar Iran Ayatullah Ibrahim Ra’esi yayin da suka je gaida jagoran a gidan s adake babban birnin Tehran.
A yayi tattaunawar su jagoran ya ja hankalin shugabannin biyu dangane da batutuwa da dama.
Jagoran ya bayyana cewa alakar dake tsakanin Iran da Siriya tana da muhimmanci gami da amfani ga kasashen biyu kuma ya bukaci a kara karfafa wannan alaka.
Jagoran ya bayyana yadda yanzu wasu kasashe wadanda a da suna cikin masu fada gami da adawa da kasar siriya amma yanzu sune kan gaba wajen bayyana shirin su na abokantaka da kasar ta siriya, dangane da wannan jagoran ya ja hankalin shugaba bashar assad kan cewa lallai a lura da abinda ya faru a baya wajen kulla alakoki.
Jagora ya bayyana cewa Janaral kasim sulaimani ya dauki kasar siriy da matukar muhimmanci, daukan da yayi mata bai gaza irin yadda ya dauki yakin kare kai na shekara takwas wanda Iran tayi da sadam husaaini ba, jagoran ya bayyana cewa ire iren su Kasim sulaimani da shahid hamedani sun dauki lamarin siriya da matukar muhimmancin da suna masa kallon wani wajibi daga cikin wajibai.
Da ya juyo bangaren dalilan da suka sabbaba samun nasarar siriyan a kan yakin da ta kara da makiyan ta ya bayyana daya daga cikin dalilin a matsayin jarumta da kuma rashin tsoron shugaba bashar assad gami da kuma gaskata Iran da yayi da dukkkan kyakykyawar niyya.
Jagoran ya bayyana cewa shugabannin wasu daga cikin kasashe sun hadu da shugabannin haramtacciyar kasar isra’ila sun sha shayi amma mutanen wadannan kasashe sun cika tituna ranar kudus ta duniya suna Allah wadarai da haramtacciyar kasar isra’ila.