Rahotanni daga Spain sun ce Barcelona ta daura aniyar kara karfin ‘yan wasanta na gaba, inda a yanzu ta zabi wasu fitattun ‘yan wasan guda hudu da ta fara tuntubar yadda za a yi ta kulla yarjejeniya da daya daga cikinsu.
Fitacciyar jaridar wasanni ta AS da ke Spain ta ruwaito cewar dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland mai shekaru 21, shi ne zabin farko da Barcelona ke son kulla yarjejeniya da shi, wanda a kakar wasa ta bana ya ci kwallaye 23 cikin wasanni 21 da ya buga.
Idan kuma har kulla yarjejeniya da Haaland bai yiwu ba, Mohd Salah na Liverpool ne zabi na 2 ga Barcelona, wanda a yanzu haka makomarsa ke cikin halin rashin Tabbas a Liverpool, la’akari da rashin kwakkwaran cigaba a tattaunawarsa da kungiyar kan bukatar tsawaita yarjejeniyarsa da ita.
Dan wasa na uku a jerin wadanda Barcelona ke fatan dauka shi ne Robert Lewandowski na Bayern Munich wanda duk da cewar shekarun sa sun ja zuwa 33, har yanzu shi ke kan gaba wajen zama mafi hatsari a gaban raga, inda a kakar wasa ta bana ya ci kwallaye 43 cikin wasanni 36. Baya ga Barcelona dai, kungiyar Paris Saint-Germain ta Faransa ma na neman kulla yarjejeniya da dan wasan.
Fitaccen dan wasa na karshe da ka iya bayyana a Barcelona kuma shi ne Romelu Lukaku na Chelsea, wanda a yanzu haka baya haskawa sosai bayan sake komawa kungiyar da yayi kan Fam miliyan 97.5.
A wani labarin kuma, mahaifin Lionel Messi ya tuntubi Barcelona game da yiwuwar dan nasa ya yi wa kungiyar kome, la’akari da cewar har yanzu bai tsaya da duga-dugansa a kungiyar PSG da ke Faransa ba.