Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da shirin kafa manya-manyan sansanonin sojinta a yankin yammacin kasar don martini ga barazanar NATO kan dauki dai-dai da ta ke yiwa kasashen gabashin Turai, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da wasu Sojin Ukraine kusan dubu 2 suka mika wuya ga Moscow.
Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce kafa sabbin sansanonin Soji wajibi ne a garesu don dakile barazanar da kasar ke fuskanta daga kungiyar ta NATO.
A wata sanarwar kai tsaye da ministan tsaron Sergei Shoigu ya yi ta gidan talabijin, ya bayyana cewa zuwa nan da karshen shekara za su samar da sansanonin Soji akalla 12 a yammacin kasar, wadanda za a wadata da manyan makaman kare kai. daga kowacce irin barazanar NATO.
Bayan matakin shugaba Vladimir Putin na aikewa da dakaru Ukraine a ranar 24 ga watan fabarairun da ya gabata lamarin da ya yamutsa zaman lafiyar duniya, matakin ya sanya kasashen Finland da Sweden da suka shafe shekaru a matsayin ‘yan ba ruwanmu neman izinin shiga NATO.
Dai dai lokacin da yakin na Rasha da Ukraine ke ci gaba da tsananta, zuwa yau juma’a akalla Sojin Ukraine 1908 suka mika wuya bayan da ma’aikatar tsaron kasar ta umarce su da su ajje makamansu don neman maslaha da Rasha.
Wasu bayanai sun ce gwamnatin Ukraine na son musayar dubunnan sojojin da Rasha ta akme mata da fursunonin Moscow da yanzu haka ke hannunta.