Bankin Duniya ya bayyana cewa sama da rabin al’ummar Falasɗinawan Gaza na dab da faɗawa cikin halin matsananciyar yunwa.
Ƙungiyar ta ƙasa da ƙasa ta ce daga cikin waɗanda za su iya faɗawa cikin wannan halin har da yara da tsofaffi.
Ƙungiyar ta yi kira da a yi gaggawar ceto rayukan Falasdinawa ta hanyar kai magunguna da abinci da sauran ababen more rayuwa a cikin gaggawa.
A watan Disambar bara bankin ya amince da dala miliyan 35 ga ƙungiyoyin agaji na UNICEF da WFP da WHO domin ayyuka a Gaza.
Waɗannan kuɗaɗen sun haɗa da dala miliyan 10 ga WFP domin ta sayi kayan abinci da kuma tukuicin kuɗi a hannu wanda za a bai wa kimanin mutum 377,000.
Sojojin Isra’ila sun sace Falasɗinawa 300 daga asibitin Gaza
Sojojin Isra’ila sun yi awon gaba da Falasɗdinawa kusan 300 a ci gaba da kutsawa da suke yi cikin asibitin Al Shifa da ke birnin Gaza.
Wata sanarwa ta ce “sojoji sun kama kusan mutum 300 tare da kawar da ƴan ta’adda da dama.
Sojojin sun kai harin ne a ranar Litinin da ta gabata, wanda ke dauke da dubban marasa lafiya da suka jikkata da kuma mazauna wurin.
A shekarar da ta gabata a watan Nuwamba, Isra’ila ta kai hari a asibitin, lamarin da ya tayar da hankalin kasashen duniya.
Tel Aviv ta yi ikirarin karya cewa mayakan Hamas na amfani da asibitin wajen ayyukan soji.
Kwanaki bayan haka ya bayyana a fili cewa sojojin Isra’ila a haƙiƙa suna magana ne a kan tudun da ke ƙarƙashin ginin da Isra’ila ta gina a shekarar 1983 a lokacin da ta yi wa Gaza mummunar mamayar
An kai Falasdinawa da suka samu raunuka, da suka hada da kananan yara zuwa Asibitin Shahidai na Al Aqsa domin kula da lafiyarsu, biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan wani gida na dangin al-Habbash a sansanin Nuseirat da ke Deir al Balah, a Gaza a ranar 19 ga Maris, 2024. / Hoto: AA
Shugabannin Amurka da Isra’ila za su gana a Washington
Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant zai gana da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin a mako mai zuwa a birnin Washington, kamar yadda wani jami’in tsaron Amurka ya tabbatar.
Jami’in, wanda ya yi magana da sharadin sakaya sunansa don bayar da cikakkun bayanai da ba a bayyana ba tukuna, ya ce Austin da Gallant suna shirin tattaunawa don ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su, da kai taimakon jinƙai ga Gaza da kuma kare wadanda ke Rafah.
DUBA NAN: Alakar Dake Tsakanin Nijar Da Rasha Da Iran, Amurka Ta Nuna Damuwa
Sama da mutum miliyan daya da suka rasa matsugunansu suna samun mafaka a kudancin birnin Gaza, inda Isra’ila ta ce tana shirin kai farmaki ta kasa.