Rahoton ya ce Craig ya kasance tun yana matashi yana gudanar da harkoki na motsa jiki, wanda hakan ya bashi damar jina gabobin jikinsa, daga lokacin kuma ya shiga safarar muggan kwayoyi.
An bankado cewa, a cikin shekara ta 1986 jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi da Amurka DEA suka kame shi, daga lokacin ne kuma bayan gudanar da bincike kan lamarinsa, suka ba shi zabi biyu, kan ko dai ya yi aiki tare da su, ko kuma ya rayu a gidan kaso, inda ya zabi yin aiki tare da su, kuma daga lokacin ne ya fara aikin leken asiri.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran alfurat News ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Usman alghanimi ya bayyana cewa, a halin yanzu jami’an tsaro sun shirya tsaf domin gudanar da ayyukan tsaro a lokacin tarukan arba’in nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ya ce halin yanzu rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta riga ta gama kammala tsare-tsarenta a bangaren ayyukan tsaro a lokacin wadannan taruka, inda jami’an dubu 20 ne aka ware domin wannan aiki.
Ministan harkokin cikin gidan na Iraki ya ce, ya zama wajibi su dauki irin wadannan kwararan matakan na tsaro, bisa la’akari da matsalolin da aka rika samu a lokutan baya na hare-haren ‘yan ta’adda lokacin tarukan addini a kasar.
Yanzu haka dai jama’a daga sassa daban-daban na kasar Iraki sun fara yin tattaki zuwa birnin Karbala domin halartar tarukan na arba’in da za su gudana a ranar 20 ga wannan wata na Safar da muke ciki