Hafsan hafsoshin sojojin Iran, Manjo Janar Mohammad Hossein Bagheri, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya janyo hatsarin jirgin saman da ya janyo mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da ministansa, Hossein Amir-Abdollahian.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran kasar, IRNA ne, ya ruwaito cewa, tawaga karkashin Birigediya Janar Pilot Ali Abdollahi, da ta kunshi kwararru na kasar da kuma na soji sun isa wurin da hatsarin ya faru a gabashin Azerbaijan, kuma tuni har sun fara gudanar da bincike.
An ruwaito labarin mutuwar manyan jami’an ne cikin tsakar daren ranar Litinin bayan sa’o’in da aka kwashe ana ta neman wajen da jirgin ya yi hatsari.
Wadanda suke cikin jirgin wanda ke komawa bayan ziyara zuwa Arewa Maso Yammacin iyakar kasar da Azerbaijan sun hada da gwamnan gabashin Azerbaijan, Janar Malek Rahmati da kuma wakilin jagoran addini na Iran a lardin, Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem.
Kamfanin dillancin labaran na Iran, ya ce nan gaba za a bayyana sakamakon binciken.
Tuni al’ummar duniya suka shiga alhinin rasuwar Shugaba Raisi.
Duniya ta dau dimi dangane da hari na farko da Kasar Iran ta kai wa Isra’ila a matsayin ramuwar gayya bayan Iran ta zargi kasar ta Yahudu da kai harin bama-bbamai da ya kashe mata manyan janar na soja da wasu kananan dakaru a ofishin jakadancinta da ke Siriya.
Hankulan kasashe sun karkata ga yadda za a shawo kan rikicin da ke neman barkewa tsakanin Iran da Isara’ila wanda ake ganin zai kara tagayyara halin da yankin gabasa ta tasakiya yake ciki na tashe-tashen hankula.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta kai harin ne a ranar Asabar da dare tare da jirage marasa matuka da makamai masu linzami akalla 300 wanda Isra’ilar ta yi ikirarin cewa ta samu nasarar tarwatsa kusa kashi 90 na adadinsu kafin su kai ga fadawa kasarta bisa amfani da na’urorin tsaron sararin samaniya bisa goyon bayan Amurka da Birtaniya.
Amma kuma Babban Hafsan Sojojin Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousabi ya ce harin na Iran ya samu gagarumar nasarar da ake bukata, kana ya ce ba za su ci gaba da kai sabbin hare-hare ba amma da Zarar Isra’ila ta yi gangancin cewa za ta rama, to kilu za ta jawo bau.
DUBA NAN: Hukumar Alhazai Ta Bayyana Lokacin Da Za’a Kammala Aiki
Harin da Iran ta kai wa Isra’ila ya haifar da zaman dar-dar a yanking abas ta tsakiya fiye da yadda aka gani tun farkon fara yakin Isra’ila da Hamas a watan Oktoba, yayin da Washington ke neman daukar matakan diflomasiyya domin sassauta rikicin yankin.