Babbar jami’ar kula da kare hakokkin bil Adam karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet yayin wani taron manema labarai biyo bayan ziyarar kwanaki shida da suka kai kasar China ta bayyana damuwa ganin irin matsakaicin hali da musulmai a yankin Xinjiang ke rayuwa.
Tsawon shekaru dai kasar ta China ta dau tsauraren matakai a kan wannan yanki,al’amarin da kungiyoyi da dama a Duniya ke ci gaba da kokawa a kai.
A wani labari na daban irnin Shanghai a China ta sanar da mutuwar mutane 39 da cutar covid-19 ta kashe a yau Lahadi, adadi mafi yawa duk da da makonni da aka shafe ana kulle, a yayin da mahukuntan birnin Beijing suka yi gargadin cewa akwai yiwuwar ta’azzarar yaduwar cutar.
Kasar, wadda ita ce ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya, tana ta kokarin shawo kan annoba mafi muni da ta addabe ta a cikin shekaru 2, inda ta yi ta kakaba dokokin kulle masu gauni, tare da gwaji ba kakkautawa.
Birnin Shanghai, wanda shine cibiyar kasuwancin China ya shiga yanayi na kulle a gaba daya watan da ya gabata, lamarin da ya sa mazauna garin zama a gida na tsawon lokaci fiye da yadda suka taba yi.
Birnin mai yawan al’umma miliyan 22, ya na ta kokarin samar da abinci mai inganci ga wadanda ke kulle a gidaje, a yayin da marasa lafiya keta korafin rashin samun kulawa, sakamakon yadda aka aike da dubban malaman lafiya zuwa cibiyoyin gwaji da kula da masu Covid-19.