Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin cewa babu wani dan Nijeriya da ya rasa ransa sakamakon yakin basasar da ake fama da shi a kasar Sudan, ta kuma bayyana cewa tuni gwamnatin Saudiyya ta fara kwashe ‘yan Nijeriya da dama ta ruwa.
Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da Karamin Ministansa, Zubairu Dada ne suka bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba.
Da yake magana kan batun da ya shafi kwashe ‘yan Nijeriya da suka makale a Sudan, Dada ya ce gwamnatin Nijeriya ta samu nasarar samun izini daga gwamnatin Sudan na kwashe ‘yan Nijeriya daga kasar.
Inda ya ce, “An fara gudanar da aikin kwashe ‘yan Nijeriya da dama domin tabbatar da tsaron lafiyarsu, abin farin ciki shi ne, kawo yanzu babu dan Nijeriya daya da ya rasa ransa. Kuma duk ‘yan Nijeriya suna cikin koshin lafiya kuma muna da kwarin guiwa da fatan cewa, babu wanda zai rasa ransa a Sudan sakamakon rikicin da ya kaure a kasar Insha Allahu”