Rahotanni sun bayyana cewa babban sakataren Janar din Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres yayi marhabin da tattaunawar da ake yi a Biyannan tsakanin Iran da kasashen turai 4 game da kasar Jamus , kuma yayi kira da a cire dukkan takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran, kamar yadda aka cimma matsaya a yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekara ta 2015 da kuma kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231.
Ya ce cirewa Iran takunkumi da aka sanya mata a bangaren mai fetur zai taimaka wajen farfado da yarjejeniyar , kuma ya bayyana takaicinsa kan yadda Iran ta jingine aiki da wasu alkwuran da ta dauka kan shirinta na nukiliya
A cikin rahoto karona 12 da ya mikawa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan batun aiki da kudurin majalisar mai lamba 2231, Guterres ya ce duk da wahalhalun da aka fuskanta game da yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar Iran , amma dai duk da haka ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen warware takaddamar
Wannan rahoton yana zuwa ne a daidai lokacin da ake zagaye na 7 a tattaunawa da ake yi a biyanna na cirewa iran takunkumin da kasar Amurka ta kakaba mata da kuma farfado da yarjejeniyar nukiliya.