Ole Gunnar Solskjaer ya ce ba kowane wasa bane Cristiano Ronaldo zai buga a tawagar Manchester United, yana mai cewa yana kokari ne ya alkinta tare da tattalin lokacin da dan wasan gaban kada a samu matsala.
Sai dai kocin dan kasar Norway ya zake cewa fa lallai ba kowane wasa ne Ronaldo zai buga ba, saboda kada ya samu matsala, duba da cewa shekarunsa 36 ne.
Solskjaer ya ce gaskiyar lamari Ronaldo yana matukar kula da kansa da lafiyarsa, saboda haka ya san ko da ya samu matsala zai murmure ba da dadewa ba, amma kamata ya yi a yi taka tsantsan.
A wani labari na daban mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce haduwarsu da Newcastle United a gobe Asabar zai zamo wasa na farko da Cristiano Ronaldo zai taka leda biyo bayan dawowarsa tsohuwar kungiyar tasa.
A shekarar 2009 ne dan wasan gaban na Portugal ya koma Real Madrid daga Manchester United gabanin barin Madrid zuwa Juventus.
Solskjaer ya bayyana cewa zai yi amfani da Ronaldo a wasan na gobe, sai dai bai yi karin bayani kan ko dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau 5 zai faro tun daga farko wasan ko kuma zai zo a sauyi ba.
Fiye da mako guda Ronaldo ya fara atisaye da ‘yan wasan Manchester United.
Bayan jerin ‘yan wasan da United ta saya ciki har da Jadon Sancho da Raphael Varane baya ga shi Ronaldo, babban aikin da ke gabanta shi ne kalubalantar takwararta Manchester City wajen lashe kofin Firimiya a cikin gida.