Babban Shugaban majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya ya ce Ayatollah Ramezani: Babban aikin da muke da shi shi ne bayyana wa daidaikun al’umma da manyan mutane na cikin al’umma da cibiyoyi na ilimi cikkakken Musulunci, kuma wajibi ne mu gabatar da addinin Musulunci ga duniya ta dukkan Fuskokinsa.
Kamfanin Dukkanin Labarai Na Ahlul Bayt (As) ABNA Ya Habarta Maku Cewar: wasu fitattun malaman addini da mabiya mazhabar shi’a daga gabashin Afirka sun gudanar da wani taro a Kampala babban birnin kasar Uganda, inda Ayatollah Reza Ramezani babban sakataren majalisar duniya ta al-Bait (AS) shi ne babban bako na wannan taro.
A cikin wannan taro, Ayatullah Ramezani ya yi ishara da wajibcin gabatar da addinin musulunci cikakke ga duniya inda ya bayyana cewa: Babban aikinmu shi ne bayyana ma daidaikun al’umma da manyan cikin al’umma da cibiyoyin ilimi game da ci gaban Musulunci, kuma wajibi ne mu gabatar da Musulunci ga duniya. ta kowace hanya. Ana kaddamar da aiyyka na kyamar Musulunci, alhali ginshikin Musulunci shi ne rahama kuma ainihin tsarin tafiyar da shugabancin Annabi (SAW) shine tafarki na kyawawan dabi’u.
Ya ci gaba da cewa: “Hakin musulmi ba shi ne ya zama magaji ba ya kama guri ya zauna a gefe ba, a’a aikinsa shi ne ya kasance a fage yana mai yin gyara da ingantawa. Kamar yadda Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi su ka ce mu kasance masu himma, da takawa, da tsafta, kuma mu san aikin da ya kan mu kuma mu aikata ayyukanmu daidai.
Babban shugaban Majalisar Duniya na Ahlul-Bait (AS) ya kara da cewa: Ba wai muna fitowa ne daga Iran domin bibiyi ayyukanda ake yi a yankunanku ba. Maimakon haka, sai dai kawai gudanar da sarrafa abubuwan suna kanku mu kuma muna tare da ku muna dafa maku. Ba mu taba neman tsoma baki ko kwace ayyukan wasu ba, amma kokarinmu kawai shi ne mu taimaka wajen kyautata yanayin mabiya Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) da shigar da Musulunci ga al’umma.
Har ila yau, a wannan taro an karrama wasu Marigayan addini tare da jawabai Mahmu Bikombo dan rikon shahid Abdulkadir da na Ahmad Nasser dan marigayi Abdullahi Nasser tare da yada faifan bidiyo na rayuwarsa.
Shi ma Hujjatul Islam wal-Muslimin Sheikh Hussain Al-Awali daya daga cikin malaman da ke zaune a kasar Uganda ya bayyana a cikin wannan taron cewa: Imani da Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) na kasashen Afirka ya samu ne dsga irin kokarin da mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu ta wannan hanya, kuma wajibi ne a gabatar da Musulunci a cikin dukkan abin da ya kamata mu kasance da tsare-tsare da kokari da ikhlasi a fagage da batutuwa manya da kanana.
A cikin wannan taro, mataimakin shugaban majalisar Ahlul Bayt (As) ta duniya a fannin kimiya da al’adu na Ahlul-Baiti, da shugaban jami’ar Ahlul Baiti, da mataimakin shugaban majalisar tattalin arziki na Ahlul-baiti sun bayyana irin ayyukan da suke gabatarwa.
Source: ABNA