Rohatanni daga kasar Kamaru na cewa akalla sojojin kasar 9 suka gamu da ajalinsu sakamakon hare-hare maban-banta da mayakan ‘yan aware dake neman ballewa don kafa jamhuriyar Ambazonia suka kaddamar a yankin arewa maso yammaci da ake amfani da turancin Ingilishi.
Yayin da a ranar Asabar wani harin kwantar bauna ya hallaka sojoji 2 a Chouame duk cikin yankin na arewa maso yamma da ake amfani da turancin Ingilishi.
Ya zuwa yanzu rundunar sojin Kamaru bata ce uffan ba, dangane da hare-haren ‘yana awaren na karshen mako a yankin da ta dauki kusan shekaru 4 tana fafatawa da ‘yan aware masu dauke da makamai dake neman ballewa domin kafa kasar Ambazonia, wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan sama da mutane 3500 ciki har da jami’an tsaro dubu 1.
Rahotanni sun ce mutane 12 aka kashe yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin fadan da akayi tsakanin bangarorin biyu dake Jihar Arewa Mai Nisa.
Gwamnan Lardin Mijinyawa Bakari yace an samu rikicin ne sakamakon gina wata madatsar ruwa da Musulmi suka yi domin taimaka musu kamun kifi a yankin da Larabawa ko kuma Shuwa Arab makiyaya ke kiwon dabbobin su.
Ba’a cika samun fadar kabilanci a kasar Kamaru ba kamar yadda ake gani a kasashen Chadi da Najeriya, musamman abinda ya shafi manoma da makiyaya.
Gwamnan yace tuni aka tura jami’an tsaro domin magance rikicin da kuma tabbatar da cewar matsalar bata yadu ba.
Gwamnan Chari-Baguirmi Gayang Souare yace wasu daga cikin Yan gudun hijirar an basu matsuguni a gidaje, yayin da wasu kuma aka aje su a makarantu da mujami’u.
Jihar Arewa Mai Nisa ta Kamaru tana kuma fama da hare haren mayakan kungiyar boko haram.