AU Ta Yaba Da Samun Ci Gaban Siyasa A Mali Da Guinea.
Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya bayyana gamsuwa da irin ci gaban yanayin siyasa da aka samu a kasashen Mali da Guinea dake yammacin Afirka.
Cikin wata sanarwar da ya fitar, Mahamat ya ce amincewa da dokar zabe a Mali, da kuma gayyatar da gwamnatin riko a Guinea, ta yiwa jam’iyyun siyasar kasar zuwa ga hawan teburin tattaunawa, sun shaida babban ci gaban da aka samu a fannin siyasar wadannan kasashe.
Jami’in ya ce a kasar Mali, amincewa da dokar zabe, ya nuna kaiwa ga muhimmin mataki na kusantar zabe.
Don haka ya yi kira ga daukacin jam’iyyun siyasar kasar da su kara rungumar tattaunawa, domin warware duk wasu banbance banbance, tare da tabbatar hade kan dukkanin sassa da lamarin ya shafa cikin harkar zaben.
READ MORE : Falasdinu; Amurka Na Rufa-rufa Akan Kisan Shireen Abu Akleh.
A kasar Guinea ma, damar da gwamnatin riko ta bayar ga jam’iyyu, ta su shiga tattaunawa, ka iya zama wata dama ta kafa ginshikin cimma matsaya kan muhimman batutuwa, Kuma bai kamata a bar irin wannan dama ta siyasa ta kubuce ba, inji shi.
READ MORE : Burkina Faso; Mutane 34 Ne Suka Rasa Rayukansu A wasu hare-Haren Ta’addaci.