Kamar yadda tarihi ya tabbatar jikan manzon Allah Imam Hussain (S.a) ya gamu da ajalin sa ne ranar goma ga watan muharran a filin karbala yayin da yake cikin matsanaciyar yunwa da kuma kishirwa, a lissafin watanni musulunci idan ranar goma ga watan muharram tayi sai afara lissafin kwana arba’in daga wannan rana domin tunawa da kwana arba’in na shahadar Imam Hussain (S.a), a kan lissafa kwanaki ashirin da suka rage a watan muharram sa’annan a lissafa kwanaki ashirin na farkon watan ashura wandacikar su ke tabbatar da zuwan ranar arba’in din Imam Hussain (S.a).
Tarihi ya tabbatar da cewa fiye da shekaru dubu ana raya wannan rana da arba’in din Imam Hussain jikan manzon Allah (S.a), kamar kowacce shekara muna cikin watan safar ne saboda haka mun fara kusantar wannan babbar rana ta arba’in din Imam Hussain (S.a) wacce zata kama ashirin ga wannan wata na safar.
Ana danganta watan safar da saukar musibobi wannan ma ta saka ake bada shawarar a yawaita addu’oi musamman ma shahararriyar addu’ar na da ta shahara ” Ya Shadidal Quwwa” wacce take maganin masibu musamman a watan safar.
Domin nuna saoyayya da kauna ga Iyalan gidan annabta al’ummu da dama su kan yin musharaka a wannan babbar ibada da tattakin arba’in wacce ta shahara kuma taron na tattakin arba’in yake zaman babban taro mafi tara al’umma a wannan karni da muke ciki.
Bana ma tattakin arba’in ya zagayo kuma ana cikin farfagandar annobar cutar korona addu’ar da al’umma suke shine Allah yasa dai kada wannan cutar ta kawo tasgwaro ga wannan babbar ibada kamar yadda a shekarar data gabata ma dai an samu babban gibi a gudanar da wannan ibada sakamakon cutar ta korona.
Wakilin mu dai ya bayyana mana yadda mutane daga sassa daban daban suka dauri aniyar musaharaka a wannan tattakin arba’in din na bana.