Arsenal ta sake farfado da fatanta na kammala gasar Firimiya ta bana a tsakanin kungiyoyi hudu na farko , abinda zai ba ta damar halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta badi, bayan doke Chelsea da kwallaye 4-2 har gida.
Yan wasan “The Gunners” da suka hada da Eddie Nketiah, da Bukayo saka da kuma Emile Smith Row ne suka taka muhimmiyar rawar ci wa Arsenal kwallaye hudun da ta lallasa Chelsea da su a wasan da suka kara a dare jiya.
Nketiah mai shekaru 22 ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea kafin daga bisani Timo Werner ya rama, Emile Smith Rowe ya sake ci wa Arsenal kwallo ta biyu, nan da nan kuma Cesar Azpilicueta ya sake ramawa Chelsea.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Nketiah ya sake cin kwallonsa ta biyu, ta amma ta uku ga Arsenal, sannan Bukayo Saka ya ci ta hudu.
Yanzu haka Arsenal tana matsayi na biyar a gasar Firimiya, bayan Tottenham ta hudu, dukkaninsu da 57-57, sai dai banbancin kwallaye, yayin da ya rage sauran wasanni shida a karkare kakar wasa ta bana.
A halin yanzu kuma maki 5 ne kawai tsakanin Arsenal da Chelsea wadad ke matsayi na uku da maki 62.
A wasu daga cikin wasannin da aka buga a jiya, Manchester City ta lallasa Brighton da kwallaye 3-0, an kuma tashi 1-1 tsakanin Everton da Leicester City.
A wani labarin na daban Kwallayen da Karim Benzema ya ci wa Real Madrid ya basu damar doke Chelsea da kwallaye 3-1, nasarar da ta sanya masu rike da kofin gasar zakarun Turai shiga tsaka mai wuyar ficewa daga gasar zakarun Turai a matakin Kwata Final.
A bangaren Chelsea, Kai Havertz ne ya rage tazarar da aka samu da kwallo 1 tilo da ya ci wa kungiyar ta sa.
Wani abu da ya dauki hankali yayin wasan dais hi ne yadda golan Chelsea Edouard Mendy ya yi kuskuren da ya baiwa Benzema damar jefa kwallo ta uku a ragarsu.
Wannan ne karo na biyu da Benzema ya ci kwallaye uku cikin wasa guda wato Hat-trick a turance, cikin gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da shi kadai ya ci kwallayen uku a karawarsu da Paris Saint-Germain a wasa na biyu na zagayen da ya kunshi kungiyoyi a gasar Zakarun Turai.
Sai a ranar 12 ga watan Afrilun nan Chelsea za ta yi tattaki zuwa birnin Madrid domin sake karawa da abokiyar hamayyar ta a karo na biyu.
Kofin gasar zakarun Turai na karshe da Real Madrid ta lashe shi ne na 13 a shekarar 2018.