Hukumar gudanarwar kungiyar Arsenal ta soma nazarin kulla yarjejeniya da tsohon mai horas da Chelsea da Inter Milan Antonio Conte domin maye gurbin kocinta na yanzu Mikel Arteta.
A baya bayan nan Jaridar UK Telegraph ta ruwaito cewa yanzu haka wasanni 5 kacal suka ragewa Arteta don ceton aikinsa na horas da Arsenal, kuma Antonio Conte tsohon kocin Inter Milan da Chelsea ke kan gaba tsakanin wadanda za su iya karbar jagorancin kungiyar ta Gunners.
A watannin baya ne dai aka rika alakanta Conte dan kasar Italiya da komawa gasar Firimiya don horas da kungiyar Tottenham Hotspur, amma yarjejeniyar ta gaza kulluwa.
Kididdiga ta nuna cewa Conte ya samu nasarar lashe wasanni 51 daga cikin 76 da ya jagoranci Chelsea a gasar Firimiya, zalika a karkashinsa ta lashe kofin kakar shekarar 2016 da 2017, kungiyar ta sallame shi a 2018.
To tun bayan wasannin karshen makon da suka gudana a gasar Firimiyar Ingila Arsenal ke shan caccaka daga magoya bayanta, masu sharhi, da kuma tsaffin ‘yan wasa ciki har da nata, sakamakon rashin nasarar da tayi da kwallaye 2-0 a hannun Chelsea.
Yayin da yake tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki, tsohon dan wasan Arsenal Bacary Sagnia da ya buga mata wasanni 284, ya caccaki dukkanin masu ruwa da tsaki a shugabancin kungiyar inda yace muddin suka ci gaba da son rai da kuma nuna halin ko in kula dangane da sayen ‘yan awsan da suka dace, to fa ba s hakkah za su ci gaba shan kaye a wassanin da ke tafe.
A cewar Sagnia abin bakin ciki ne ganin yadda kimar tsohuwar kungiyarsa tasa ya zube duk da irin ficen da tayi a zamanin su da kuma na wadanda suka gabace su.
Sai dai kocin Arsenal Mikel Arteta ko a jikinshi wai a tsikari kakkausa, domin kuwa yayin martini kan caccakar da ake musu cewa yayi, ko da wasa bai damu da bacin rai ko sukar kowa ba kan rashin nasarar da suka yi a wasansu da Chelsea.
A cewar mai horaswar abinda yake bukata shi ne ‘yan wasan da za su fuskanci kalubalen da ke gabansu tare da kawo karshensa.
A ranar 28 ga wannan watan Arsenal za ta kara da Manchester City.