Idan aka ce Tsayuwar Arfa, ba ana nufin mutum ya yi ta tsayawa ne kyam, babu zama, babu hutawa, babu kwanciya ba, a’a, ko mutum barci yake yi a filin Arfa to yana daga cikin tsayuwar Arfan.
An karɓo Hadisi daga Jabir (RA) Annabi (SAW) ya ce “Babu wasu kwanaki masu daraja da girma a wajen Allah da suka fi kwana goma nan na farkon watan Sallar Layya”.
A cikin kwanakin ne ake hawa Arfa a ranar 9 ga wata, ranar 10 ga wata ake gudanar da sauran manyan ayyukan Hajji irin su Jifa, Hadaya, Aski da ɗawaful Ifada. Kuma a rannan ne sauran Musulmi a duk inda suke a duniya suke yin Sallar Idi da taya Alhazai yanka da liyafar taya su murnar sun yi Hajji lafiya.
Wasu Malamai sun yi bayanin cewa hatta kwana 10 na ƙarshen watan Ramadan ba su kai waɗannan kwanaki goman ba. Shi ya sa yin azumi a cikinsu ga wanda ba ya Aikin Hajji, da yin nafilfilin dare suke da ɗimbin falala.
Wani mutum ya tambayi Annabi (SAW) cewa “Kwana 10 ɗin nan sun fi hatta yaƙin tsayar da Tafarkin Allah da ake cewa wanda ya mutu a ciki ɗan Aljanna ne, wanda ya dawo – da rai – zai dawo da lada mai yawa?”. Annabi (SAW) ya ce “Eh, sun fi yaƙin tsayar da Tafarkin Allah.”
Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren waɗannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”. Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a hulɗar da ke tsakaninmu ba.
Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a riƙa fassarawa da yadda ƙananan ƙwaƙwalenmu ke ɗaukawa ba. Duk wanda ya ce zai fassara da ƙaramin hankalinsa, to wannan ya sa wasa a cikin sha’anin Allah (SWT).
Hadisin ya ci gaba da cewa “Ubangiji yana sauka a saman duniya sai ya yi alfahari da mutanen doron ƙasa. Yana kallon mutanen yana wa Mala’iku alfahari da su cewa ku kalli bayina, sun zo mun da birkitaccen gashi masu ƙura-ƙura, ga su sun yini, sun zo mun daga nesan duniya suna neman rahamata, ba su ga azabata ba.” Munzir ya ce Abu Ya’ala, Bazzaru, Ibn Khuzaima da Ibn Hibban suka ruwaito Hadisin. Amma lafazin da aka ruwaito da shi kuwa, na Ibn Mubarak ne daga Safyanus Sauri, shi kuma daga Zubairu bin Aliyin daga Anas bin Malik (RA).
Ma’anar kai ya yi ƙura-ƙura, ko da gashin mutum bai yi ƙura ba, Allah zai ba shi ladan, shi dai ya kasance ya kiyaye abubuwan da Shari’a ta ce ma sa kar ya yi. A kan haka ne ya sa ba a so a riƙa yin kwalliya bayan wanda aka yi a yayin ɗaukan harami.
Annabi (SAW) ya ce ba a taɓa ganin wata ranar da ake ‘yantar da bayi daga barin shiga wuta kamar Ranar Arfa ba. Duk zunubin da aka yi a shekara, rannan Allah yana zubar da shi.
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji
An karɓo kuma daga Ibn Mubarak, daga Safyanus Sauri, daga Zubairu bin Aliyin, shi kuma daga Anas bin Malik (RA) ya ce, “Annabi (SAW) ya tsaya a Arfa, da rana ta kusa faɗuwa, sai Annabi ya kira Bilalu ya ce ya sa mutane su yi shiru zai yi magana, sai Bilalu ya tashi ya ce wa jama’a; ku yi shiru ga Annabi (SAW). Sai Annabi (SAW) ya tashi yana kan raƙumi ya ce, “Ya ku taron mutane, yanzu Jibrilu ya zo mun ya gaishe ni, ya ce Ubangijina ya gafarta wa duk waɗanda suka zo Arfa ɗin nan, da waɗanda duk suka zo Mina (Mash’aril Harami) kuma Allah ya lamunce musu duk laifin da ke kansu”. Sai Sayyidina Umar bin Khaɗɗab (RA) ya miƙe ya ce “Ya Ma’aikin Allah, wannan namu ne da muka zo wannan Hajjin kawai? Sai Annabi (SAW) ya amsa ma sa da cewa “Naku ne kuma da duk waɗanda za su zo Arfa a bayanku har tashin ƙiyama”. Sai Sayyidina Umar (RA) ya ce “Alherin Allah yana da yawa kuma ya yi daɗi”. Imam Muslim da waninsa suka ruwaito.
Har ila yau, an karɓo wani Hadisin daga Ummul Mu’umina Aisha (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wata rana da Allah yake yawaita ‘yanta bayinsa daga wuta kamar Ranar Arfa. Ubangiji yana kusantowa (SWT) ga mutane har ya yi wa Mala’iku alfahari da su ya ce, “Me waɗannan mutane suke so ne?”.
Wannan yana nuna tambayar ta jindaɗi ce (yadda ya dace da Allah), saboda ai ya san abin da kowa yake so amma kuma sai ga shi (SWT) yana tambayar Mala’iku. Haƙiƙa ba ƙaramar falala ba ce a ce Allah ya yi alfahari da mutum, Alhamdu Lillah.
An karɓo Hadisi daga Abu Darda’i (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Babu wata rana da ake ganin Shaiɗan a matsayin mafi ƙasƙanci da wulaƙanta da tunkuɗewa da fushi kamar Ranar Arfa”. Ba komai ya jawo ma sa wannan ba sai abin da yake gani na Rahamar Allah da take sauka.
Hatta shi kansa Shaiɗan yana zuwa Arfa, a maimakon shi ma ya samu yafiya a wurin Allah, sai kuma ya sake jibgan wani laifin saboda hassada a kan Rahamar da Allah yake wa bayinsa. Yana-ji-yana-gani, Allah zai yafe wa al’umma duk saɓon da ya ingiza su suka aikata.
Wannan baƙin cikin ma bai isa ba, tun da har ya yi hassada, ya ji baƙin cikin gafarar da Allah ya yi wa bayinsa, za a kuma tafi Mina bayan an sauko daga Arfa a jefe shi a can.
Ko kuma dama shi duk mai hassada idan ya ga wanda Allah ya baiwa ni’imar da yake baƙin ciki a kai; sai ya ji rashin lafiya ta taso ma sa. Abin da yake samun Iblis kenan. Al’umma za su taso daga Arfa cikin gafara kuma su je su jefe shi.
Haka nan, ya yi irin wannan baƙin cikin Ranar Badar. Da aka tambayi Annabi (SAW) irin baƙin cikin da ya yi a ranar, Annabi (SAW) ya ce “Iblis da ya ga Jibrilu yana jagorantar Rundunar Mala’iku, ba a taɓa ganin tsoro ya kama shi irin na rannan ba, har ma ya mance ya ce yana tsoron Allah”.
DUBA NAN: Makarantar Kano Poly Tayi Gobara A Safiyar Talata
Allah ya amfanar da mu baki ɗaya, Albarkar Annabi (SAW).