A yayin wata tattaunawa da suka yi da Kamfanin Dillancin Labarai Na Abna masanan sun tabbatar da cewa: Arbaeen Wani Yunkuri ne na shirya zukata don bayyanar Imamul Mahdy As.
Masana biyu daga kasar Turkiyya da suka halarci taron “Tasirin Ilimi na Arbaeen” na kamfanin dillancin labarai na Ahl-Bait (AS) na gidan yanar gizo, sun bayyana ra’ayoyinsu game da wannan lamari na duniya.
Ga yadda tattaunawar ta su ta gudana kamar haka:
Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA: tattakin Arbaeen wani lamari ne na shirya zukata don bayyanar Imamul Mahdy As Wannan lamari mai girma ya sanya ayar tambaya ga al’ummar duniya, shin menene musabbabin faruwar wannan lamari kuma me ya sa kuma ga wanene aka fi yin taron mutane mafi girma a duniya?
Da alama Imam Husaini (AS) ya gabatar da kansa ga duniya da Arbaeen ne sannan Imam Asr (AS) ma zai samu gabatar da kansa ga mutanen duniya ne ta hanyar Imam Husaini (AS).
A ci gaba da gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin na Ahlul Baiti (AS) na kamfanin dillancin labarai na Abna, a yayin taron Arba’in na Husaini, malaman jami’o’i biyu daga kasar Turkiyya sun tattauna kan batun Arba’in da abubuwan da suka faru a cikinsa.
Dokta Javad Gok masani kuma manazarci kan lamurran siyasa da zamantakewa dangane da alakar Arbaeen da bayyanar Imamul Hujjah As ya ce: Imamai Ma’asumai (a.s) sun ba da kulawa ta musamman ga tattakin Arbaeen na Husaini, ta yadda Imam Hassan Askari (As) ya sanyata amatsayin daya daga cikin alamomin mumini guda biyar, sun gaskata, domin wannan al’amari yana da muhimmanci. A dunkule, aikin Ziyarar Arbaeen wani nau’i ne na share fage wajen bayyanar Imamuz Zaman (AS).
Maziyarta su yi tunanin cewa Imam Mahdi (A.S) ya bayyana a Makka kuma magoya baya da ‘yan Shi’a sun je su taimake shi a inuwar Imam Husaini (A.S.). Wani abin al’ajabi ne, Ance Imam Husaini (a.s.) ya na karbawa dansa Imam Zaman (a.s.) bai’a ne daga ‘yan Shi’a da masu ibada a lokacin ziyarar Arba’in.
Sananne ne a wajen kakansa mai girma Imam Hussain (a.s.). Don haka kafin bayyanarsa Imam Hussaini (AS) ya kasance sananne ga duk duniya.
Ya ce dangane da irin girman wannan waki’a: A tattakin Arbaeen, dukkanin mutane daga kasashe daban-daban da tunani mabanbanta suna taruwa a karkashin tutar Imam Husaini (AS). Sun fito ne daga dukkan kungiyoyin Musulunci, hatta wadanda ba musulmi ba da kiristoci suna zuwa Karbala.
A lokacin aikin Hajji wanda daya ne daga cikin manya-manyan al’amura a kasashen musulmi, mutane miliyan biyu da rabi zuwa uku ne ke taruwa a birnin Makka, amma a lokacin Arba’in, Maziyarta tsakanin miliyan 25 zuwa 27 ne ke taruwa a Karbala, kuma wannan bai taba faruwa a ko’ina a duniya wanda hakan ke nuna karama ce.
Duk mai son ganin mu’ujizar Ubangiji to ya zo ya ziyarci Arbaeen. Sama da ninki 10 ne na al’ummar Karbala ke taruwa a lokacin Arba’in, kuma wannan shi kansa abin mamaki ne. Wannan ba zai yiwu ba sai a Karbala. Idan kuna son ganin albarkar abin duniya da na ruhi, ku zo Karbala.
Wannan manazarci kan lamurran siyasa da zamantakewa, ya yi nuni da cewa Arba’in share fage ce na zuwan Imamul Hujja As, ya shawarci maziyarta da cewa: Ina rokon dukkan masu ziyara da su dukufa wajen ganin sun gaggauta zuwan Imam Zaman (AS) a lokacin ziyarar Arba’in.
Dr. Mahmoud Ajar, malami a jami’ar Koniya da ke kasar Turkiyya, shi ma wani bako ne na wannan gida, wanda ya yi bayani kan abubuwan da suke jayo hankali da kyawun Arbaeen.
Ya ce: Bisa kididdigar da hukuma ta yi, mutane miliyan 20 zuwa 30 ne ke halartar aikin ziyarar Arbaeen, wanda ya zamo babu iriin wannan taron.
Jama’a daga bangarori daban-daban na Musulunci, ‘yan’uwa Ahlus Sunna da ma wadanda ba musulmi ba, suna zuwa aikin ziyarar Arba’in, me ake nufi da Ziyarar Arba’in? Menene zai iya zama falsafar wannan babban aikin ibadah? Wannan tambaya ce mai mahimmanci da yakamata muyi tunani akai.
Dangane da darussan Arbaeen kuwa ya ce: Idan aka ambaci sunan Ziyarar Arbaeen, abin da ya fara zuwa a zuciyar mutum shi ne yaki da tsayuwa gaban zalunci. Duk wadanda suka je aikin ziyarar Arbaeen, hakika sun koyi ma’ana da manufar fada da zalunci da azzalumai kuma sun fahimci wannan gwagwarmaya ta wata fuska. Ya kamata wanda ya je aikin ziyarar Arbaeen ya koyi falsafar da dalilin da ya sa Imam Husaini (a.s) ya yi wannan yunkuri kuma akan wane irin zaluncin ne yayi gwagwarmaya.
A halin yanzu, akwai manyan laifuka da ke faruwa a duniya, wanda Amurka da Isra’ila suka goyi bayansu. A kasashen Siriya da Iraki da Yemen da sauran kasashen musulmi, za ka ga bama-bamai da makami mai linzami suna kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, kuma kasashen masu girman kai ne suke aikata wannan ta’asa.
Me ya kamata a yi a kan wadannan ta’addanci? Wasu suna ganin ya kamata mutum yayi shiru ya hada kai da Amurka da sahyoniyanci! Shin da gaske wannan shine mafita da yaki da zalunci? Tabbas wannan ba shine mafita ba kuma ba zai taba kasancewa ba. Mafita daya daga cikin ayoyin kur’ani mai girma ita ce a tashi tsaye wajen yakar zalunci da azzalumai, wanda dole ne a yi a daidaiku da kuma a kungiyance, kuma wannan shi ne sakon Imam Husaini (a.s.).
A karshe farfesa na jami’ar Koniya ya ce: Ku kula, mutane miliyan 20 zuwa 30 ne ke zuwa wannan aikin ziyara suna aiwatar da wannan fahimtar gwagwarmaya da yunkuri, kuma daga nan ne suka fahimci sakon Imam Husaini (AS) kuma wannan yana da alaka kai tsaye ga mas’alar fitowar Imam Zaman (AS). Ya kamata ’yan Adam su kasance a kusa da Imamin zamaninsu ta wannan hanyar su taimake shi.
Source: ABNA