Tsohon sojan ya yi murabus daga mukaminsa a watan Afrilu na shekarar 2019 bayan da sojoji suka yi watsi da shi sakamakon makonni na zanga – zangar adawa da shirin sa na tazarce a karo na biyar.
A wani labarin nadaban kotun daukaka kara ta soji a Algeria ta wanke dan uwa kuma tsohon mai ba da shawara ga hambararren shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika da wasu tsoffin shugabannin hukumar leken asiri biyu, wadanda aka yanke wa hukuncin shekaru 15 a kurkuku bisa laifin yin zagon kasa ga sojoji da kuma gwamnati.
Baya ga Said Bouteflika, janarori Mohamed Mediène, da Athmane Tartag, da kuma wata ‘yar gwagwarmayar Louisa Hanoune, wadanda aka yanke wa hukunci a wannan shari’ar, kotun daukaka karar ta wanke su.
A wani labarin kuma, ma’aikatar tsaron Algeria tabbatar da mutuwar sojojinta biyu da mahara masu ikirarin jihadi 4, bayan wani kazamin fafatawa a yankin Tipaza dake Yammacin Alger.