Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ci gaba da fuskantar matsin lamba bayan kungiyarsa ta yi canjaras babu ci tsakaninta da Cadiz a jiya a gasar La Liga ta Sifaniya.
Koeman ya yi korafi kan jan katin da alkalin ya ba shi, yana mai cewa, kasar Spain ne kawai ake irin wannan hukuncin babu gaira babu dalili a cewarsa.
Yanzu haka wasannin La Liga biyu kacal daga cikin biyar Barcelona ta samu nasara, lamarin da ya dada zafafa hasashe game da makomar Koeman.
Ba a dai sani ba ko Koeman zai ci gaba da jagorancin kungiyar kafin nan da ranar Lahadi mai zuwa, ranar da Barcelona za ta yi wasanta na gaba da Levante a gida.
A wani labari na daban mujallar Fobes ta rawaito cewa, Cristiano Ronaldo na Manchester United ya yi wa Lionel Messi na PSG fintikau, inda a yanzu ya dare duk wani dan wasan kwallon kafa a duniya wajen samun albashi mafi tsoka.
Dan wasan zai samu Dala miliyan 70 daga albashinsa da kuma kudaden alawus-alawus da Manchester United za ta ba shi.
Sauran kudaden za su fito ne daga kamfanonin da dan wasan ke yi musu tallace-tallace kamar Nike da Herbalife da sauransu.
Mujallar ta Forbes ta ce, Ronaldo na cikin sharaharrun ‘yan wasa a duniya, inda yake da mabiya fiye da miliyan 500 a shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma Twitter.