Antonio Guterres ya ce Musulmai da dama ba za su yi bukukuwan ƙaramar Sallah ba sakamakon yaƙi da yunwa a duniya.
An kashe fiye da mutum 13,000 sannan aka raba sama da mutum miliyan 8 da gidajensu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma rabin ƴan ƙasar su miliyan 25 suna buƙatar agajin jinkai.
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce zuciyarsa ta “karaya” sanin cewa Musulmai da dama a Gaza da Sudan da ma wasu ƙasashe ba za su samu damar yin bukukuwan ƙaramar Sallah ba sakamakon yaƙi da matsananciyar yunwa.
“Duk shekara, ina mika saƙon taya murna ga Musulmai a faɗin duniya na ƙaramar Sallah,” in ji Guterres a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.
Ya ƙara da cewa, “Zuciyata ta karaya sanin cewa a Gaza, da Sudan da wurare da dama — Musulmai da dama ba za su iya gudanar da bukukuwan sallah ba saboda yaƙi da yunwa.”
Sudan ta faɗa cikin yaƙin basasa sakamakon arangamar da ake yi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun sa-kai na Rapid Support Forces (RSF) tun watan Afrilun bara.
An kashe fiye da mutum 13,000 sannan aka raba sama da mutum miliyan 8 da gidajensu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma rabin ƴan ƙasar su miliyan 25 suna buƙatar agajin jinƙai.
Isra’ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 33,000 tun ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da ƙungiyar Hamas ta kai mata harin ba-zata wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla 1,200.
DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya Za Ta Sa Kafar Wando Daya Da Masu Digirin Bogi
Kazalika dakarun Isra’ila sun lalata galibin gine-ginen da ke Gaza sannan suka tilasta wa Falasɗinawa sama da miliyan 1.9, inda suka faɗa cikin yunwa da ƙunci.