Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sauka a Najeriya domin ziyarar kwanaki 2.
Bayan saukarsa, Antonio Guterres ya ziyarci jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar, yankin. da har yanzu kef ama da matsalar hare-haren mayakan Boko Haram da na ISWAP da suka balle daga kungiyar.
Yayin ziyarar tasa a Borno, sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya gana da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum a birnin Maiduguri, daga bisani kuma ya gana da wasu daga cikin iyalan da rikicin Boko Haram ya shafa tsawon fiye da shekaru 10.
Daga jihar ta Borno, Antonio Guterres ya tashi zuwa birnin Abuja, inda zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.
A birnin na Abuja ana sa ran Guterres ya jagoranci wani bikin alhini da kuma karrama wadanda suka rasa. rayukansu yayin harin bam din da aka kai kan ginin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2011. Daga nan kuma zai gana da wakilan kungiyoyin mata da matasa, da kuma shugabannin addinai da ‘yan jarida.
Wannan dai shi ne karo na farko da Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ke ziyartar Najeriya tun bayan hawansa kan mukamin.
A wani labarin na daban Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce watakila yayi ritaya idan ya bar kungiyar da ta zama zakarar gasar La-Liga a bana, sai dai ya ce a shirye yake ya cigaba da zama tare da Madrid din tsawon shekaru masu yawa a nan gaba.
Ancelotti dan kasar Italiya mai shekaru 62 a dunIya, ya zama koci na farko a tarihi da ya lashe kofunan manyan lig-lig guda biyar na Turai, nasarar da ya cimma a wannan kakar tare da Real Madrid bayan lashe gasar La Liga, inda kuma zai jagoranci karawa da Manchester City ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun Turai.
Yanzu haka dai Kocin dan kasar Italiya yana yarjejeniya da Real Madrid har zuwa shekarar 2024, bayan da ya koma kungiyar a karo na biyu a shekarar bara daga kungiyar Everton.
Yayin wata zantawa da manema labarai ne kuma, Ancelotti ya ce zai iya cigaba da horas da Real Madrid tsawon shekaru 10, idan kungiyar ta bukaci hakan.