Ansarullah; Sojojin Kasashen Waje Sun Dukufa Wajen Satar Danyen Man Fetur Da Gas Na Kasar.
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen AbdulMalik Huthi ya fadawa tashar talabijin ta Almasira ta kungiyar a jiya Talata kan cewa sojojin kasashen yamma suna kwasar arzikin man fetur da gas na kasar kamar yadda suke so.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah Abdulmalik Huthi ya na cewa sojojin kasashen waje wadanda suka hada da na UAE da Saudia da kuma na kasashen Amurka da Burtani su na da hannu a wawuce arzikin man fetur da gas na kasar Yemen.
A shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudia da kawayenta na kasashen larabawa kimani 10 suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.
Amma bayan ta kasa yin haka har bayan shekaru 7 da fafatawa da mutanen kasar, a halin yanzu sojojin wadan nan kasashe sun koma bangaren satar danyen man fetur da gas na kasar, a dai dai lokacinda mafi yawan mutanen kasar suna fama da karancinsa tun farkon yakin.
Labarin ya kara da cewa hatta bayan yarjejeniyar tsagaita budewa juna wutan wanda bangarorin biyu suka amince tare da shiga tsakani na MDD, sojojin kawancen Saudia suna hana jiragen ruwa dauke da makamashi isa tashar jiragen ruwa ta Hudaita don amfanin mutanen kasar.