Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce watakila yayi ritaya idan ya bar kungiyar da ta zama zakarar gasar La-Liga a bana, sai dai ya ce a shirye yake ya cigaba da zama tare da Madrid din tsawon shekaru masu yawa a nan gaba.
Ancelotti dan kasar Italiya mai shekaru 62 a duniya, ya zama koci na farko a tarihi da ya lashe kofunan manyan lig-lig guda biyar na Turai, nasarar da ya cimma a wannan kakar tare da Real Madrid bayan lashe gasar La Liga, inda kuma zai jagoranci karawa da Manchester City ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun Turai.
Yanzu haka dai Kocin dan kasar Italiya yana yarjejeniya da Real Madrid har zuwa shekarar 2024, bayan da ya koma kungiyar a karo na biyu a shekarar bara daga kungiyar Everton.
Yayin wata zantawa da manema labarai ne kuma, Ancelotti ya ce zai iya cigaba da horas da Real Madrid tsawon shekaru 10, idan kungiyar ta bukaci hakan.
A wani labarin na daban Tarayyar turai ta bukaci mambobinta da su shirya wa yiwuwar yankewar samar da iskar gas daga Rasha, inda ta zake a kan cewa ba za ta bada kai bori ya hau ba a kan bukatar Rasha ta a biya ta da kudin rubles.
An jiya a yau Talata Tarayyar Turan za ta gabatar da wani sabon kunshin takunkumai da zummar hukunta shugaba Rasha sakamakon mamayar Ukraine da ta yi, ciki har da takunkumi kan sayen danyen manta.
Rasha ta bukaci abokan huldarta daga kasashen da ba sa jituwa, kuma suke sayen gas a hannunta da su biya da kudinta na rubles, a wani yunkuri na rage radadin takunkumin da aka kakaba mata a bangaren hada hadar kudade, kuma a halin da ake ciki, ta katse aikewa da gas kasashen Bulgaria da Poland biyo bayan bijire wa bukatarta.
Tarayyar Turai da Amurka ba su ji dadin mamayar da Rasha ta wa Ukraine ba, lamarin da ya sa suka yi ta kakaba mata takunkumai a bangarori dabam dabam.