Sabon binciken da aka gudanar ya tabbatar da zargin da akeyio na hannun hukumar leken asirin ingila dumu dumu a kisan babban janaral din jamhuriyara musulunci ta Iran, janaral kasim sulaimani wanda aka kashe a wani harin tsoro da aka aiwatar a babban birnin kasar Iraki, Baghdad.
Rahotanni suna tabbatar da cewa da yiwuwar an samu nasarar kashe janaral kasim sulaimani ne bayan anyi amfani da bayanan sirri da aka samu daga kafar leken asiri ta ”Menwith Hill intelligence” wacce ke karkashin sojin marautautar ingila, kamar yadda jaridar Guradian ta rawaito a ranar asabar din da ta gabata.
Yiwuwar hannun ingila a cikin wannan mummunan aiki na kisan babban kwamandan sojin Iran din babban abin tsoro ne saboda hakan na iya sabbaba yaki musamman lura da yadda iraniyawa ke son janaral din nasu, kuma a bangaren ingila da kasa fitowa fili ta musznta zargin da akayi mata, kamar yadda wani babban dan jarida a ingila ya fada.
Su dai jami’an leken asiri na ”Menwith Hill” ana zargin su da cewa sun bada gagarumar gudunmawa a aiyukan kashe wasu manya a kasar yemen kuma hakanan ake da kwakwkwaran zargin suna da hannu dumu dumu a kisan janaral kasim sulaimani kamar yadda jaridar Guadian din ta rawaito.
Menwith Hill dai itace babbar tashar bayanan sirri dake karkashein NSA, mai ayyukan ta a kasashen duniya kuma tana da ma’aikata sama da 600 amurkawa a yayin da take da sama da ma’aikata 500 mutanen ingila a matsayin fararen hula amma suna aiki da kafara ta leken asiri.
Ministan harkokin wajen Iran dai ya tabbatar da cewa dole za’a hukunta masu hannu a kisan janaral kasim sulaimani.
An dai kashe janaral kasim sulaimani ne a wata ziyara da ya kai kasar iraki bisa gayyatar sa da gwamnatin kasar tayi kuma a tare dashi a kwai irakawa da harin ya rutsa dasu ciki har da babban na hannun daman sa Abu Mahdi Almuhandis.
Bayyanar wannan bayanan sirrin dai ya sanya kungiyoyin kare hakkin dan adam sun tsananta kiraye kirayen su na a gaggauta hukunta masu hannu a kisan janaral kasim sulaimani din.