Ana zanga-zanga bayan ɗan siyasa mai ƙyamar musulmi ya ƙona Al Kur’ani a Sweden.
Mummunan rikici ya barke a kasar Sweden a makon nan a birnin Linköping da ke gaɓar tekun gabashin ƙasar, inda aka yi arangama tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga da suka fito domin nuna fushinsu kan ƙona Al Kur’ani mai tsarki da wani dan siyasa mai tsaurin ra’ayi ya yi a wani gangaminsa.
Rahotanni sun ce ƴan sanda uku suka jikkata.
Mutane sun sake fitowa zanga-zangar, a cewar hukumomin birnin Orebro da ke tsakiyar kasar, bayan wani gangami na nuna ƙyamar baƙi da kuma addinin Islama ƙarƙashin jagorancin mai tsattsauran ra’ayi Rasmus Paludan ɗan siyasa mai asali biyu Denmark da Sweden. A yayin zanga-zangar ‘yan sanda tara suka jikkata.
An kama mutum biyu a lokacin zanga-zangar. Ƴan sanda sun nuna cewa aikinsu shi ne su tabbatar da ƴancin mutane na bayyana ra’ayinsu, don haka ba haƙƙinsu ba ne su zaɓi wanda yake da gaskiya.
READ MORE : Macron ya soki manufar Le Pen ta haramta wa matan Musulmi yin lulluɓi.
Baludan ya daɗe yana haifar da ruɗani da ce-ce-ku-ce. A watan Nuwamban 2020, hukumomin Faransa sun kama shi tare da korarsa daga ƙasar.
READ MORE : Saudiyya ta buƙaci limamai su daina tsauwalawa a addu’ar Al-ƙunutu na sallolin tahajjud.