Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Tarukan Ranar Quds Da Nuna Goyon Baya Ga Falastinu.
A cikin wannan mako ana ci gaba da gudanar da taruka da gangami a kasashen duniya daban-daban domin nuna goyon baya ga al’ummar falastinu.
Tarukan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da manyan taruak da jerin gwano na ranar Quds ta duniya a Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma.
An gudanar da irin wannan taron da aka fara a jiya a birnin Tehran ta hanyar hotuann bidiyo, wanda manyan malamai da fitattun ‘yan gwagwarmayar muslunci na yanki da kuma na Falastinu suka gabatar da jawabai.
Daga wadanda suka gabatar da jawabai akwai Sayyid Hassan nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah, sai kuma Isma’il Haniyya shugaban kungiyar Hamas, da Ziyad Nakhala shugaban kungiyar Jihad Islami, da kuma sheikh Alsumaidai, shugaban malaman ahlu sunnah na kasar Iraqi da dai sauransu.
A nata bangaren Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta fitar da sanarwa inda ta jaddada cewa masallacin Aqsa yana matsayin jan layi ga musulmi.
Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kula da harkokin Falastinu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi, wanda aka shirya domin kare Quds da Falastinu, wanda ya samu halartar daruruwan fitattun malaman addinin Islama da magoya bayan Falastinawa daga kasashe 40, Khaled Mashaal ya ce dabarun makiya yahudawan sahyoniya sun ginu ne a kan mamayar yankunan Falastinu, Kuma gwamnatin yahudawan ta kowace hanya tana kokarin kammala yakin a masallacin Aqsa.
Mashal ya bayyana cewa al’ummar Falastinu da suka dogara da hakkinsu a birnin Kudus da kuma masallacin Al-Aqsa, sun yi jarumtaka wajen nuna adawa da zaluncin haramtacciyar kasar Isra’ila, tare da tabbatar da cewa wannan masallaci na musulmi ne kawai, kuma yahudawa ba su da wani hakki a kansa.
Ya bayyana cewa, duk da rashin daidaiton da ke tsakanin Falastinawa da yahudawa, da zalunci da fin karfin da ake nuna wa Falastinawa, amma al’ummar Falastinu sun nasara wajen hana tabbatar manufar yahudawan, wato shafe Falastinu daga doron kasa.
Mashal ya ce: abin da ya faru a baya-bayan nan a masallacin Aqsa, wasu gungun matasa Falastinawa masu fafutuka a masallacin Aqsa, wadanda suka tashi tsaye a madadin al’umma baki daya, don kare alkiblar musulmi ta farko.
Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a wajen Falastinu ya jaddada cewa, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar da cewa rayuwa ta hakika tana nufin rayuwa karkashin tutar sadaukarwa da tsayin daka domin kare karamar al’umma da kuma wurarenta masu tsarki.