Wata mummunar zanga-zanga ta barke a garin Corsica na Faransa sakamakon zargin da jama’a ke yi kan cewa ana cin zarafin Dan gwagwarmayar kwato hakkin dan adam din nan dake tsare a gidan yari tun shekarar 2003 wato Yvan Colonna.
Al’ummar garin na wannan zanga-zanga ne don nuna fushin su game da cin zarafin dan gwagmayar kwato hakkin Dan adam Yvan Colonna wanda ana tsare dashi a gidan yari tun shekarar 2003.
Tun farko dai an yanke masa hukuncin daurin rai da rai ne sakamakon kama shi da hannu a kisan magajin garin wato Corsica, Calude Erignac, bayan lakada masa duka, abinda ya yi sandiyyar shigar sa dogon suma kafin daga bisani ya mutu a ranar 2 ga watan Maris din 1998 wannan shekara.
Yvan wanda ke tsare a wani gidan yari dake Kamaru kuma jama’ar garin na samun labarin cewa yana fuskantar muzgunawa da kuma cin zarafi a gidan yarin, abin da ya tashi zanga-zangar.
Tun farko dai a cewar kafafen yada labaran cikin gida jama’a sun fusata ne bayan samun rahoton Mutuwar Yvan saboda karancin Iska wadda aka hana shi da gan-gan a gidan yarin, sai dai kuma daga baya hukumomin gidan yarin sun musanta batun mutuwar tasa.