An Zabi Tsohon Shugaban Kasar Somalia A Matsayin Sabon Shugaban Kasa.
Majalisar dokokin kasar Somalia ta zabi tsohon shugaban kasar Hassan Sheikh Maahmood a matsayin sabon shugaban kasar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa HassanSheikh Mahmood dan shekara 66 a duniya ya sami nasara a kan shugaban kasa mai ci Muhammad farmajo a zagaye na ukku na zaben da majalisar dokokin kasar ta gudanar a jiya Lahadi.
Kafin Haka Hassan ya taba zama shugaban kasar ta Somaliya tsakanin shekaru 2012-2017, inda ya sami amincewar yan majalisa 214-sannan Farmajo ya sami 210.
An sanadar da sakmakon zaben a tsakiyar daren jiya Lahadi, sannan masu goyon bayansa sun fito daga wurin taron suna ihu da harba bindiga a sama.
A jawabinsa na Farko bayan zabensa, sabon shugaban kasar ya bayyanancewa babu daukar fansa a kan yan siyasar da suka saba masa.
READ MORE : Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Jerin Gwanon Tunawa Da Ranar Al-Nakba A Kasashen Duniya.
A halin yanzu dai akwai manya-manyan al-amura guda biyu a gaban shugaba Hassan, wadanda kuma sune samar da tsaro mai dorewa a kasar da kuma karancin ruwan da ya jawo mummunan fari a kasar.
READ MORE : Iran; Kasashe Masu Karfi Na Amfani Da Hakkin Dan Adam Wajen Cimma Muradun Siyasa.