An Yi Jerin Gwanon Tir Da Isra’ila A Wasu Kasashen Duniya.
Yayin da farmakin da jami’an tsaron Isra’ila ke kaiwa a masallacin Quds, ke kara tsananta, an yi jerin gwanon tir da cin zarafin da Isra’ilar ke yi wa falasdinawa a harabar masallacin al-Aqsa da sauran wurare a yankunan da ta mamaye.
Dubban jama’a a kasashen duniya da dama ne suka fito kan tituna domin nuna bacin ransu dangane da cin zarafin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawan a masallacin al-Aqsa, a yayin da kuam manyan kasashen duniya sukayi gum da bakunansu kan lamarin.
A Pakistan dubban mutane ne suka gudanar da jerin gwano bayan sallar Juma’a a manyan biranen kasar, inda suka yi Allah wadai da farmakin da Isra’ila ta kai kan Falasdinawa masu ibada a Masallacin na Al-Aqsa, tare da yin kira ga kasashen musulmi da su tsawata cikin gaggawa domin kare wannan wuri mai alfarma da kuma rayukan Falasdinawa.
An kuma gudanar da irin wannan jerin gwanon a biranen Lahore, Karachi, Peshawar, Dhaka, da dai sauransu, domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.
Masu zanga-zangar dai sun yi ta rera taken nuna adawa da gwamnatin Isra’ila tare da yin kakkausar suka ga America da gwamnatocin kasashen yammacin duniya kan goyon bayan da suke baiwa ‘yan mamaya.