Sauran sojojin 2 kuwa, sune wadanda aka yankewa daurin tsawon shekaru 20 akan fyaden da suka yiwa mata a ranar 31 ga watan Maris, a dai garin na Minembwe.
Gabashin lardin Kivu na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, dai ya dade yana fama da tashin hankali, sakamakon rikici tsakanin ‘yan kabilar Banyamulenge, ‘yan Tutsi da ke kasar ta Congo amma ‘yan asalin Rwanda, da kuma sauran kabilun da ke yankin, kan ikon mallakar filaye da sarrafa albarkatun kasa.
A wani labarin na daban kalla mutane 22 aka kashe a wani sabon rikicin da ya barke a yankin arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.
Kazalika an kashe takwas daga cikin mayakan da suka kawo farmakin a cewar rahotanni.
Desire Maldora, wani shugaban kungiyar fararen hula ya ce, mutane 15 suka mutu a lardin Djugu tsakanin ranakun Jumu’a da Asabar a fafatawar da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan tawayen na CODECO.
Kungiyar ta CODECO mai dauke da makamai, na ikirarin samar da kariya ga ‘yan kabilar Lendu.
Kungiyar dai daya ce daga cikin kungiyoyi fiye da 120 na ‘yan tawaye masu cin karensu babu babbaka a yankin gabashin Jamhuriyar Congo, kuma akasarinsu sun kafu ne a sakamakon yake-yaken da aka yi fama da su fiye da shekaru 50 da suka gabata.