An Shiga Kwana Na Ashirin Na Rikicin Rasha Da Ukraine.
An shiga kwana na shirin na rikicin Rasha da Ukraine, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa sojojin Rashar sun fara kai hare hare kan wasu unguwanni da ke tsakiyar kyiv babban birnin kasar Ukraine.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran komawa bakin tattaunawa karo na hudu yau Talata, tsakanin Rashar da kuma Ukraine.
A wanann Talata kuma wata tawagar kungiyar tarayyar turai, da ta hada da Fira Ministan Poland, da Slovenia zasu isa a birnin Kyiv don nuna goyon bayan EU da kuma ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
READ MORE : Rasha Da Ukraine Zasu Sake Tattauanwa Yau Litini.
Ko a yau ma an bude hanyoyin jin kai don kwashe fararen hula daga garuruwan Sumy, Konotop, Trostianets da Lebedine.
A jiya Litinin, motoci 160 ne suka samu damar barin birnin Mariupol.