An Shiga Kwana Na 16 Na Rikicin Rasha Da Ukraine.
An shiga kwana na sha shidda na matakin sojin da Rasha ke cewa tana dauka kan Ukraine.
A halin da ake ciki dai kwamitin tsaron MDD, zai yi wani zama yau Juma’a, bisa bukatar da Rasha ta gabatar, bisa zargin Amurka da taimakawa Ukraine hada makammai masu yada kwayoyin cuta, batun da Kiev Da Washington ke musantawa.
A wani batun kuma shugabanni da gwamnatin kasashen turai na wani taro a Versailles domin nazarin matakan dauka na rage dogaro da man fetur da gaz na Rasha, da kuma kara taimakawa Ukraine.
Kafin hakan dai Rasha ta sanar da kakaba takunkumi kan fitar da kayayakin noma da na kiwon lafiya da fasaha da kuma kayan wutar lantarki har zuwa karshen wannan shekara, a matsayin maida martani kan takunkuman da kasashen turai suka kakaba mata.
A cewar MDD, sama da mutane miliyan biyu ne suka tsare wa rikicin na Ukraine, ciki kuma har da yara miliyan daya a cewar kungiyar Save The Children.
READ MORE : Putin Ya Ce Ana Samun Ci Gaba A Tattaunwar Da Ake Da Ukraine.