Shugaban kotun koli na kasar Guinea, Mamadou Sylla ya rantsar da Mamady Doumbouya, wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaba, Alpha Conde a ranar 5 ga watan Satumba.
Shugaban rikon kwaryan bayan rantsar dashi ya bayyana manufofinsa, inda ya yi alkawarin cewa, babu wani daga cikin wadanda suka jagoranci juyin mulkin da zai tsaya takarar shugaban kasar karkashin mulkin farar hula.
An gudanar da Bikin rantsar wa din ne a Juma’ar nan da ya kasance jajibirin bikin tunawa da ranar samun ‘yancin kan Guinea daga Faransa, a filin taro na Muhammed-V da ke Conakry.
A wani labarin na daban tawagar shugabannin kungiyar kasashen yammacin Africa ECOWAS/ CEDEAO ta gana da jagororin da suka kwace mulki a kasar Guinea domin gabatar ma su da sakon kungiyar na neman soja su gaggauta mka mulki cikin watanni shida.
Tawagar ta kunshi Shugaba Nana Akufo-Ado na Ghana da Shugaban Cote d’Ivore Alassane Ouattara sun gana da shugabannin sojan Guinea ne a wani Otel dake birnin Conakry.
Da isarsu Otel din ne kuma jagoran sojan na Guinea da suka kwace iko a Guinean Lt. Col Mamady Doumbouya ya isa otel din cikin wata motar soja mai sulke, tare da rakiyar sojoji da suka rufe fuskokinsu.
Ganarwar dai sun yita ne bayan da Kungiyar ta ECOWAS ta ja kunnen sojan da suka kifar da Gwamnatin farar hula ta Alfa Conde, ranar 5 ga wannan wata da muke ciki, da su hanzarta mika mulki.
Kazalika kungiyar ta kirba masu haramcin tafiya, ga kuma toshe asusun kudadensu da kaddarorin kasar.
Juyin Mulki sojan na Guinea ya jefa shakku cikin dorewar democradiya a wasu kasashen Africa da har yanzu ake samun juyin mulkii da rana tsaka.